Babban Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (Federal Fire Service – FFS), Samuel Adeyemi Olumode, ya miƙa sakon taya murna na Kirsimeti ga ‘yan Najeriya a duk faɗin ƙasar nan, inda ya yi musu fatan alheri, farin ciki, zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin iyalai da al’umma.
A cikin sakonsa na wannan lokaci, Babban Daraktan ya bayyana Kirsimeti a matsayin lokaci na haɗin kai, tunani da kyakkyawar mu’amala, tare da tunatar da ‘yan ƙasa muhimmancin ɗaukar nauyin bai ɗaya wajen tabbatar da tsaro a cikin gidaje da al’ummomi.
CGF Olumode ya jaddada cewa tsaro nauyi ne na kowa da kowa, musamman a lokacin bukukuwa inda ayyuka ke ƙaruwa, yana kira ga ‘yan ƙasa da su kasance masu lura da duk wani haɗari tare da bin matakan tsaro domin hana afkuwar gobara da sauran gaggawa da za a iya kauce musu.
Ya kammala da yi wa ‘yan Najeriya fatan Kirsimeti cikin kwanciyar hankali da kuma sabuwar shekara mai albarka, yana mai jaddada ƙudirin Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi a lokacin bukukuwa da ma bayan haka.


