Jami’an Special Mining Marshals sun sake tabbatar da cewa ingantaccen tsaro ba ya takaita ga amfani da karfi kawai. A Karamar Hukumar Mariga ta Jihar Neja, Hukumar ta samu gagarumar nasara ta hanyar dabarar sulhu da hadin kan al’umma domin magance matsalolin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da suka dade suna addabar yankin.
Kwamanda ACC Attah John Onoja ya bayyana cewa wannan mataki ya yi daidai da tsarin aiki na Marshals, wanda ke mayar da hankali kan warware rikice-rikice ta hanyar nazarin yanayin kowace matsala sannan a zabi mafita da za su kare muradun dukkan bangarorin da abin ya shafa.
Abin da ya faru a Mariga ya nuna muhimmin darasi ga tsarin tsaro a Najeriya: tattaunawa mai ma’ana, gina amana, da samar da hanyoyin magance matsaloli na gida na iya haifar da dorewar zaman lafiya a wuraren da amfani da karfi ka iya kasa cimma nasara. Nasarar Mining Marshals ta kara tabbatar da muhimmancin dabarar tsaro mai sassauci wacce ke dogara da bayanan sirri wajen kare fannin ma’adinai na kasa.
Hukumar ta kuma shawarci al’ummar yankin da su ci gaba da amfani da damar zaman lafiya da aka samu, domin inganta kare muhalli da kuma bunkasar ci gaban yankin baki daya.



