Ma’aikatar Raya Ma’adinai ta ƙaryata zargin da Kwamitin Wucin Gadi na Majalisar Wakilai kan Binciken Hakko Ma’adinai, Tsaro da Hana Saƙaƙen Kuɗi ya yi, cewa ma’aikatar ta gaza yin haɗin kai da binciken da ake gudanarwa kan hakko ba bisa ka’ida ba a fadin ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Mukaddashiyar Sakatariyar Dindindin ta Ma’aikatar, Vivian Okono, ta bayyana cewa zargin da Shugaban Kwamitin, Sanni Abdulraheem, ya yi ba su da tushe, kuma ba su nuna gaskiyar yadda ma’aikatar ke hulɗa da majalisar ba.
A ranar Laraba, Mista Abdulraheem ya gayyaci Ministan Ma’adinai, Dele Alake, da Darakta-Janar na Hukumar Rijistar Ma’adinai ta Ƙasa, yana zargin cewa hukumomin biyu na nuna rashin sha’awar yin aiki tare da kwamitin duk da muhimmancin rawar da suke takawa wajen gyare-gyaren da ake nema domin kawar da hakko ba bisa doka ba.
Ya kuma zargi ma’aikatar da hukumar MCO da rashin mayar da martani kan sahalewar da kwamitin ya nuna tun farko, yana mai cewa hakan yana jinkirta cigaban binciken.
Sai dai Madam Okono ta musanta zargin, tana mai cewa bayanan kwamitin sun bata hakikanin abin da ya faru. Ta ce ma’aikatar ta kasance tana aiki cikin gaskiya tare da riƙe hanya mai buɗe ido ga majalisar.
Ta bayyana cewa tawagar ma’aikatar ta shirya halartar zaman kwamitin a ranar Talata, 18 ga Nuwamba, kamar yadda wasikar farko ta nuna. Amma daga baya sai ma’aikatar ta samu sakonni masu karo da juna daga sakatariyar kwamitin.
Madam Okono ta ce domin kauce wa rashin fahimta, ta kira Magatakardar Kwamitin, Ademola Adewale, a ranar Litinin, 17 ga Nuwamba, domin tabbatar da lokacin zama. An shaida mata an daga zaman daga ƙarfe 10:00 na safe zuwa 2:00 na rana washe garin.
Amma daga baya a ranar, ma’aikatar ta sake tuntubar magatakardar, inda aka sanar da ita cewa kwamitin ya ɗage halartar ma’aikatar har sai wani lokaci da za a sanar.
“Saboda waɗannan dalilai, gayyatar gaggawa da kwamitin ya ce ya aikawa ma’aikatar ba ta da wani muhimmanci,” in ji ta.
Mukaddashiyar Sakatariyar Dindindin ta jaddada cewa ma’aikatar na da kyakkyawar alaƙa da Majalisar Wakilai da kwamitocinta, tana mai cewa bangarorin zartarwa da na majalisa suna da nauyin haɗa kai domin cimma muradun ‘yan Najeriya.





