An samu mummunan lamari a ranar Alhamis a unguwar Oba Ile da ke cikin Karamar Hukumar Akure North ta Jihar Ondo, inda wani matashi mai shekaru 19 da ke fama da matsalar tabin hankali ya kashe jami’in Hukumar Tsaro ta Najeriya (NSCDC) ta hanyar caka masa wuka.
Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa mahaifiyar wanda ake zargin ita ce ta kira jami’an NSCDC domin su taimaka su daure ɗanta, wanda ya fara tayar da hankali tun da sassafe. Rikicin ya ɓarke ne lokacin da jami’an suka yi ƙoƙarin daure matashin domin ya daina cutar da jama’ar unguwa.
Wani ganau ya bayyana cewa a lokacin fafutukar daure shi, matashin ya rinjayi ɗaya daga cikin jami’an NSCDC, ya karɓe wukarsa sannan ya caka masa. Duk da cewa jami’in yana ɗauke da bindiga, ba zai iya kare kansa ba saboda ruɗani da tashin hankali.
“Abin takaici ne,” in ji gan-da-ido. “Ko da yake jami’in na da bindiga, bai iya shawo kan lamarin ba kafin matashin ya kai masa hari.”
Jami’in Hulɗa da Jama’a na NSCDC a Jihar Ondo, Daniel Aidamenbor, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa abin ba daɗi ba ne kwata-kwata. Ya bayyana cewa jami’in ya kasance cikin yunƙurin kai matashin zuwa cibiyar jinya ne lokacin da abin ya faru.
Haka kuma, Jami’in Hulɗa da Jama’a na ‘Yan Sandan Jihar, Olayinka Ayanlade, ya tabbatar da cewa jami’in NSCDC ya rasu a asibiti sakamakon raunukan da ya samu yayin artabu da wanda ake zargi.
An tsare matashin yayin da bincike kan lamarin ke ci gaba.




