Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa shugaban Ƙungiyar ‘Yan asalin Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, hukuncin daurin rai-da-rai.
A yayin da take yanke hukunci a ranar Laraba, Mai Shari’a James Omotosho ya bayyana cewa an yanke wa Kanu hukuncin daurin rai-da-rai kan tuhume-tuhumen lamba ɗaya, biyu, huɗu, biyar, da shida, inda kotun ta zaɓi wannan hukunci maimakon hukuncin kisa.
Kotun ta kuma yanke masa daurin shekaru 20 kan tuhume-ta uku, da kuma ƙarin shekaru biyar kan tuhume-ta ta bakwai, ba tare da wani zabin biyan tara ba.
Mai Shari’a Omotosho ya yanke hukuncin ne bayan ya tabbatar da Kanu da laifi kan dukkan tuhume-tuhume bakwai da ake masa na laifukan ta’addanci.





