Mai girma Ministan Ayyuka, Injiniya Dave Umahi, ya bai wa Hukumar Tsaro ta Fararen Hula (NSCDC) reshen Jihar Lagos wani sabon jirgin ruwa domin karfafa ayyukan kare muhimman gine-ginen gwamnatin tarayya, ciki har da gadar Third Mainland da sauran manyan gadar ruwa a fadin jihar.
A karkashin umarnin Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, hukumar ta Lagos a ranar Alhamis, 20 ga Nuwamba 2025, ta fara aiwatar da matakan da aka cimma tare da Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (ONSA). Matakan dai sun hada da karfafa hadin gwiwa da Hukumar Ruwa ta Kasa (NIWA) da Ma’aikatar Ayyuka domin dakile ayyukan barna da ke barazana ga muhimman gine-ginen gwamnatin tarayya.
Kwamandan NSCDC na Jihar Lagos, Mista Keshinro Adedotun, ya bayyana godiya ga Ministan Ayyuka bisa goyon bayansa, yana mai cewa gudummawar jirgin ruwan ta kara wa jami’an da ke yaki da ayyukan bata gari a karkashin gada kwarin gwiwa.
A yayin taron, kwamandan ya kaddamar da sabon jirgin ruwan tare da bude sabon Sashin Tsaro na Ruwa da Kariya ga Muhimman Gine-ginen Kasa. Haka kuma ya jinjinawa tsohuwar Babbar Kwamandar Ayyuka ta Tarayya a Lagos, Injiniya (Hajiya) O.I. Kesha, bisa jajircewarta wajen ganin hukumar ta samu dukkan kayan aikin da take bukata domin tabbatar da tsaron gadar Third Mainland da sauran gine-ginen tarayya a jihar.
Sabon kwamandan Sashin Tsaro na Ruwa da Kariya ga Gine-ginen Kasa, ACC Oloyede Emmanuel Ige, ya nuna godiyarsa ga Ministan Ayyuka, Babban Kwamandan NSCDC, da kuma Kwamandan Jihar Lagos. Ya yi alkawarin gudanar da aiki tukuru wajen tabbatar da tsaro, sintiri, da sa ido a dukkan hanyoyin ruwa da ginshikan gwamnati da ke fadin Lagos.
Kafa wannan sashi na musamman zai kara karfin tsaro wajen kare muhimman gine-ginen kasa daga barazanar barna kamar su haramtacciyar hako kasa, tono-tuno ba bisa ka’ida ba, lalata gine-gine, da kuma mamaye filayen gwamnati. Jirgin ruwan da aka baiwa hukumar zai taimaka matuka wajen dakile hako kasa ba bisa ka’ida ba wanda kan iya kawo barazana ga gadoji da tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.
Yayin zantawa da manema labarai a taron, kwamandan Lagos ya gargadi masu lasisin hako kasa da su kiyaye dokoki yayin gudanar da ayyukansu. Ya kuma ja kunnen masu aikata haramtacciyar hako kasa, mamaye filaye, da tono-tuno su daina ko kuma su shirya fuskantar hukunci mai tsanani idan an cafke su.





