Commandant Muhammad Kabiru Ingawa fitaccen ƙwararren jami’in tsaro ne kuma gogaggen mai gudanarwa wanda aikinsa ya nuna hazaka, gaskiya da cikakkiyar jajircewa ga hidimar kasa.
Ɗan asalin Karamar Hukumar Ingawa ta Jihar Katsina, yana zuwa NSCDC Jihar Jigawa da zurfin ƙwarewa da ya tara a tsawon shekaru a wurare da bangarori daban-daban na Hukumar.
Commandant Ingawa shugaba ne mai kuzari da hangen nesa, wanda ya taba jagorantar NSCDC Jihar Nassarawa a matsayin State Commandant, inda ya yi fice wajen gudanar da ayyuka cikin tsari da kwarewa. Haka kuma ya yi hidima a jihohin Katsina, Jigawa, Delta da Nassarawa, sai kuma Ofishin Yanki na Kaduna, inda ya shugabanci sashen Intelligence and Investigation da kuma Anti-Corruption and Transparency Unit — mukamai da suka kara zurfafa kwarewarsa a fannin tsaro, bayanan sirri da kuma inganta da’a a ma’aikata.
Dawowarsa NSCDC Jihar Jigawa ana daukarta a matsayin dawowar gida, kasancewar ya taba shafe kusan shekaru shida yana aiki a jihar a baya. Wannan ya ba shi cikakkiyar fahimta game da tsarin tsaron jihar, wanda hakan ya shirya shi wajen jagorantar daidaitacciyar tsaro mai ma’ana, mai hangen nesa, tare da kusanci ga al’umma.
Commandant Ingawa ya kammala karatun digirinsa na farko a Jami’ar Bayero Kano (BUK) a fannin Business Administration. Haka kuma mamba ne mai ƙima a Corporate Institute of Administrators. Ya halarci manyan kwasa-kwasai na horo, ciki har da Basic Training a makarantar horon Nigeria Correctional Service da ke Owerri, Imo State, da kuma Advanced Training a Nigeria Correctional Service Staff College, Kaduna.
A shekarar 2013, an karrama shi da Most Punctual Staff Award daga NSCDC Jihar Jigawa—lambar yabo da ta nuna ladabi, jajircewa da tsantsar kishinsa ga aiki.
Kafin shigarsa cikin Corps, Commandant Ingawa ya yi aiki da tsohuwar DNCR (wacce yanzu ta koma NIMC) sannan ya ci gaba zuwa Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya, inda ya yi aiki a matsayin Assistant Coordinator kuma ya taka rawar gani wajen aiwatar da ayyukan raya yankunan karkara.
Commandant Muhammad Kabiru Ingawa mutum ne na iyali, yana da mata daya tare da albarkar ‘ya’ya bakwai. Kwarewarsa, jagorancinsa da kishinsa ga aiki suna kara karfafa gwiwar al’umma yayin da yake karɓar sabuwar rawar da zai taka a matsayin 13th Substantive Commandant na NSCDC Jihar Jigawa.



