Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da cewa an kashe sojoji biyu da mambobin Civilian Joint Task Force (CJTF) biyu bayan ‘yan Boko Haram sun yi wa dakarun 25 Task Force Brigade kwanton bauna a yayin sintiri a yankin Wajiroko da ke Azir Multe, Karamar Hukumar Damboa a Jihar Borno, a daren Juma’a.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, Mataimakiyar Daraktan Hulda da Jama’a ta Sojojin Najeriya, Lt.-Col. Appolonia Anele, ta bayyana cewa an kai harin ne yayin da dakarun ke dawowa daga nasarar sintiri a dajin Sambisa. Ta ce tawagar sintirin, karkashin jagorancin Brigadier General M. Uba, ta yi karfi da karfe har ta fatattaki maharan da karin karfin makami.
Anele ta tabbatar da cewa sojoji biyu da mambobin CJTF biyu sun rasa rayukansu a yayin gumurzun, inda ta ce rundunar sojin ta mika ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da tunawa da sadaukarwarsu ga kasa. Ta kuma karyata jita-jitar da ke yawo cewa an yi awon gaba da Kwamandan Brigaden, tana mai cewa labarin karya ne.
Shugaban Rundunar Sojin Kasa, Lt.-Gen. Waidi Shaibu, ya yaba da jarumtaka da jajircewar dakarun, yana tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da murkushe ta’addanci. A watan da ya gabata ma, wani harin Boko Haram a Jihar Borno ya kashe Lt.-Col. Aliyu Paiko, Kwamandan 202 Tank Battalion, tare da wasu sojoji a yankin Kashimri na Karamar Hukumar Bama.



