Kwamandan Rundunar NSCDC Special Mining Marshals, ACC John Onoja Attah, ya sake samun girmamawa a matakin ƙasa.
a wannan karon a matsayin “Nation Builder for Protection Against Illegal Mining” a bikin 3rd Nigeria’s Nation Builders Annual Awards da aka gudanar a Abuja.
A wurin Mining Marshals, wannan lambar yabo ba wai ado ba ne kawai. Shaidar ce ta jajircewa, sadaukarwa, da himmar da ACC Attah ke nunawa wajen jagorantar yaki da fasa-kaurin ma’adinai a fadin ƙasar nan.
An shirya taron ne ta hannun National Civil Society Coalition (NACCSO) tare da hadin gwiwar Vision-One Leadership Development Initiative, domin karrama mutanen da ayyukansu ke taimakawa wajen gina Najeriya mafi inganci da cigaba. Shugaban NACCSO, Emmanuel Johnny, ya yabawa ACC Attah kan “gwagwarmaya mai cike da jarumtaka da rashin gushewa” wajen kare dukiyar ma’adinai da a da ake wawashewa — ƙoƙarin da ya ce ya taimaka wajen “juyar da asarar kudaden shiga na Najeriya zuwa riba.”
A jawabinsa, ACC Attah ya mika wannan girmamawa ga Commandant General na NSCDC, Farfesa Abubakar Ahmed Audi, tare da gode wa Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, da Ministan Ma’adinai, Dr. Dele Alake, bisa goyon bayansu. Ya jaddada cewa aikinsu a bayyane yake: sanya bukatar kasa kafin ta kowa.
Sauran fitattun wadanda suka samu lambar yabo sun hada da:
• Janar C.G. Musa (rtd), tsohon CDS
• Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, Shugaban NECO
• Silas Agara, Darakta Janar na NDE
• CP Ifeanyi Henry Uche, Shugaban Police National Cybercrime Centre
• Hajiya Aisha Ahmed Audi, Shugabar CDOWA
Duk da yawan lambobin yabo da ake bayarwa a Abuja, wannan karramawar ta musamman ce ga Mining Marshals. Tana tabbatar da cewa karkashin jagorancin ACC John Onoja Attah, yaki da fasa-kaurin ma’adinai ba kawai ana gani ake yi ba yana canza tsarin wani bangare da a da aka san shi da isa da rashin bin doka.



