Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da cewa an sako Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Muhammad Sama’ila Bagudo, wanda aka sace mako guda da ya gabata.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Nafiu Abubakar, ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa an sako dan majalisar ne da yammacin ranar Asabar, 8 ga Nuwamba, misalin ƙarfe 8:00 na dare, bayan ya shafe sama da mako ɗaya a hannun masu garkuwa da mutane.
An sace Bagudo ne a ranar 31 ga Oktoba, 2025, a yankin ƙaramar hukumar Bagudo ta jihar. Abubakar ya ce bayan an sako shi, an kai shi asibiti domin duba lafiyarsa, sannan daga baya ya haɗu da iyalansa lafiya.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Kotarkoshi, ya yaba da haɗin kai da jarumtar jami’an tsaro da suka shiga aikin ceto, inda ya bayyana su a matsayin jarumai masu ƙwarewa da ƙwazo.
Sanarwar ta ce: “Rundunar ’yan sanda ta yaba da ƙarfin hali, jajircewa, da ƙoƙarin hadin gwiwar jami’an tsaro da aka tura wajen aikin bincike da ceto, haka kuma muna godiya ga al’ummar Jihar Kebbi da suka bayar da muhimman bayanai da suka taimaka wajen samun nasarar sako ɗan majalisar cikin koshin lafiya.”
Rundunar ta kuma jaddada aniyarta na ci gaba da kai hare-hare kan masu aikata laifukan garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran manyan laifuka a jihar.
An kuma roƙi mazauna jihar da su kasance masu natsuwa da lura, tare da kai rahoton duk wani mutum ko motsi da suka zarga zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa ko wani ɓangare na tsaro domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.
Sace Mataimakin Kakakin ya tayar da hankula a fadin Jihar Kebbi, amma sakin sa lafiya ya kawo farin ciki da natsuwa ga iyalansa, abokan aikinsa, da masu wakiltarsa.





