Hoto: Daga hagu: Dr. Usman Jahun da Isiaka Mustapha yayin miƙa wasikar nadin kyauta a Fadar Gwamnati, Dutse, Jihar Jigawa, jiya.
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya karɓi takardar gayyata daga masu shirya 2025 People’s Security Monitor Annual Security Summit & Recognition Award, inda aka kuma naɗa shi don samun lambar yabo ta People’s Security Monitor Grand Award, tare da gayyatarsa a matsayin Bakon Girmamawa (Chief Guest Speaker). An miƙa wasikar gayyatar ne ta hannun Isiaka Mustapha, Babban Jami’in Gudanarwa kuma Babban Editan People’s Security Monitor, inda Dr. Usman Muhammed Jahun, Mai Baiwa Gwamna Shawara kan Harkokin Tsaro, ya karɓa a madadin Gwamnan a Fadar Gwamnati, Dutse.
A cikin jawabinsa, Isiaka Mustapha ya bayyana cewa taron zai gudana a ranar Laraba, 10 ga Disamba, 2025, a Nigerian National Merit Award House, Maitama, Abuja. Ya ce an zabi Gwamna Namadi saboda irin rawar da yake takawa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da ci gaban al’umma a Jihar Jigawa. Mustapha ya yaba da salon jagorancin Gwamnan na haɗin kai da kuma yadda yake aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro wajen tabbatar da daidaito da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Da yake mayar da martani a madadin Gwamnan, Dr. Usman Jahun ya gode wa masu shirya taron bisa ganin bajintar Gwamna Namadi wajen inganta tsaro da kyakkyawan shugabanci. Ya tabbatar da cewa Gwamnan zai halarci taron tare da gabatar da jawabin sa na musamman. Ana sa ran taron na shekara-shekara zai tara manyan hafsoshin tsaro, masu tsara manufofi, sarakuna, da shugabannin kungiyoyin fararen hula daga sassa daban-daban na ƙasa domin tattauna sabbin dabaru wajen ƙarfafa zaman lafiya, tsaro, da cigaban kasa mai ɗorewa.



