Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) ƙarƙashin jagorancin CC EA Ajayi ta ci gaba da nuna ingantaccen jagoranci ta hanyar haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki, shirye-shiryen samar da zaman lafiya, da kuma kyakkyawar alaƙa da al’umma.
An karrama Kwamandan da Kyautar Jakadan Zaman Lafiya daga Cibiyar Zaman Lafiya ta Arewa (Northern Peace Foundation) a matsayin yabo kan gagarumin gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban al’umma, raya zaman lafiya, da inganta tsaro a fadin Jihar Sokoto.
An gudanar da bikin bayar da kyautar a Hedikwatar NSCDC ta Jihar Sokoto a ranar Talata, 4 ga Nuwamba, 2025, da misalin karfe 3:00 na rana, tare da halartar manyan jami’an hukumar.
Kwararre Yahusa Abdullahi, wanda shi ne Koodinetan Cibiyar Zaman Lafiya ta Arewa, ne ya mika kyautar ga Kwamandan Jihar, tare da lambar shaidar shiga kungiyar da kuma mujallar shekara ta 2025 ta cibiyar.
A wani bangare, DCC M.S. Buda, daya daga cikin manyan jami’an hukumar wanda ke jagorantar sashen DPRS, shima an bashi Kyautar Jakadan Zaman Lafiya saboda jajircewarsa wajen bautar kasa da kokarinsa na wanzar da zaman lafiya, hadin kai da daidaiton al’umma.
Karkashin jagorancin CC EA Ajayi, hukumar ta karfafa hadin kai da masu ruwa da tsaki a matakin ƙananan hukumomi, tare da inganta rabon bayanan leken asiri tsakanin jami’an hukumar da al’umma.
Ta hanyar haɗin gwiwar cibiyoyi da hukumomi, hukumar ta kara karfin martani kan kalubalen tsaro da ke tasowa a jihar, abin da ya haifar da ƙarin amincewar jama’a da ingantaccen tsarin gargadi da kuma shiga tsakani daga al’umma kan batutuwan tsaro.
Salon jagorancin CC Ajayi na buɗaɗɗen ƙofa ya ƙara jawo amincewar jama’a, tare da sanya NSCDC ta Sokoto zama cibiyar da ake ganin mai gaskiya, amana da kwarewa a cikin hukumomin tsaro.
Koodinetan Cibiyar Zaman Lafiya ta Arewa, Comrade Yahusa Abdullahi, ya nuna godiya ga hukumar NSCDC ta Sokoto bisa gaskiya, amana, da jajircewarta wajen tabbatar da kyakkyawar suna ga hukumar a idon jama’a.
A jawabin karɓar kyautarsa, CC EA Ajayi ya jaddada muhimmancin zaman lafiya a tsarin tsaro na jihar, inda ya bayyana cewa dorewar zaman lafiya na bukatar cikakkiyar haɗin kai da al’umma da ke inganta ci gaban zamantakewa da jinƙai domin dorewar rayuwar ɗan Adam.
A zamanin mulkinsa, hukumar ta samu nasarori masu yawa a fannin ci gaban tattalin arziki, rabon bayanan tsaro daga al’umma, da rage barazanar tsaro. Haka kuma, ya inganta kare muhimman kadarorin kasa, ya karfafa haɗin kai da sauran hukumomin tsaro, tare da rage rikice-rikicen manoma da makiyaya a yankunan karkara.



