Sabon Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Muhimman Ababen Gwamnati (NSCDC) na Jihar Jigawa, Kwamanda Muhammad Kabiru Ingawa, ya mika Takardar Karɓar Aikin sa ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi (FCA), a fadar Gwamnati dake Dutse.
A yayin wannan ziyarar, Kwamanda Ingawa ya bayyana godiya mai zurfi ga Gwamnan bisa irin goyon bayan da Gwamnatin Jihar ke ci gaba da bai wa hukumar NSCDC. Ya tabbatar da aniyarsa ta ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumar da Gwamnatin Jihar, musamman a fannoni na tsaro, kare muhimman kayan gwamnati da na ƙasa, kula da bala’o’i, da kuma haɗin kai da al’umma.
Kwamanda Ingawa ya tabbatar wa Gwamnan cewa, a karkashin jagorancinsa, hukumar za ta ƙara ɗaukar matakai masu ƙarfi wajen yakar laifuffuka irin su lalata kayan gwamnati, hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, satar shanu, da sauran miyagun ayyuka da ke iya kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban jihar. Ya jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da aikinta cikin ladabi, ƙwarewa, da sadaukarwa, don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar Jigawa.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya tarbi sabon kwamandan da farin ciki tare da taya shi murna bisa nadin da aka yi masa. Gwamnan ya tabbatar da kudirin gwamnatinsa na ci gaba da haɗin kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake morewa a fadin jihar. Ya yaba wa hukumar NSCDC bisa irin rawar da take takawa wajen tabbatar da tsaro a matakin al’umma, tare da tabbatar wa da ita goyon bayan gwamnati wajen aiwatar da aikinta yadda ya kamata.
Mika takardar karɓar aiki ta nuna fara cikakken wa’adin aiki na Kwamanda Muhammad Kabiru Ingawa a matsayin Kwamandan NSCDC na 11 da aka tabbatar a Jihar Jigawa.




