Sabbin shugabannin rundunonin tsaro da majalisar dattawa ta tabbatar da su a ranar Laraba sun bayyana sabbin dabarun da za su bi wajen shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya. Sun jaddada muhimmancin karfafa hukumar ‘yan sanda, bunkasa samar da kayan yaki a cikin gida, da kuma hadin kai tsakanin hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Babban Hafsan Tsaro na Kasa (CDS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kara tallafa wa rundunar ‘yan sanda ta kasa, domin sojoji su mayar da hankali kan aikin kare iyakokin kasa daga barazanar waje.
“Idan an karfafa ‘yan sanda, rundunar soji za ta mayar da hankali kan kare kasa da yaki da ta’addanci,” in ji shi, yana mai jaddada cewa yaki da rashin tsaro aikin kowa ne dan kasa.
Janar Oluyede, wanda a baya ya kasance Babban Hafsan Sojin Kasa (COAS), ya kuma bukaci karin kudaden aiki ga rundunonin tsaro da kuma mayar da hankali wajen kera kayan yaki a cikin gida, yana gargadin cewa dogaro da kayan waje ba zai dore ba.
“Najeriya dole ta gina karfinta wajen fuskantar barazanar ta’addanci da satar bayanai ta intanet. Idan ba mu koyi dogaro da kai ba, matsalolin za su ci gaba,” in ji shi.
Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Laftanar Janar Olufemi Oluyede (CDS), Rear Admiral Idi Abbas (Shugaban Rundunar Sojin Ruwa), da Air Marshal Sunday Kelvin Aneke (Shugaban Rundunar Sojin Sama) bayan amincewa da kudurin da jagoran majalisa, Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti Central), ya gabatar.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yabawa kwarewar Janar Oluyede wajen jagoranci, yana mai cewa: “Kai ne Janar wanda yake jagoranci daga gaba. Tun da ka hau kan mukami, babu wani yanki da tutar Boko Haram ta sake bayyana. Ka ceci kasa daga barazanar da dama.”
Shugaban Sojin Ruwa, Rear Admiral Idi Abbas, ya nuna rashin amincewa da shirin kafa hukumar Nigerian Coast Guard, yana mai cewa hakan yin kwafi ne da aikin da rundunar ruwa ke yi.
“Ba mu bukatar wata sabuwar hukuma da za ta yi aiki irin namu. A maimakon haka, a baiwa rundunar ruwa rabin kudin da ake shirin baiwa Coast Guard domin karfafa mu,” in ji shi.
Abbas ya bayyana cewa rundunar ruwa tana amfani da drones da sabbin kayan fasaha wajen yaki da satar danyen mai da matsalolin tsaro a teku.
“Yawanci satar mai tana faruwa a wurare masu wahalar isa. Tare da amfani da na’urorin leƙen asiri da kyakkyawan sufuri, za mu fi iya sa ido da yin martani cikin sauri,” in ji shi.
Ya kara da cewa an kafa Ofishin Ayyukan Musamman (Special Operations Command) a Makurdi, Jihar Benue, domin kare hanyar Benue–Lokoja da hanyoyin ruwa na cikin kasa.
Game da sake shigar da tsofaffin ‘yan ta’adda cikin al’umma, Abbas ya ce dole a tafi a hankali tare da tuntubar wadanda suka rasa ‘yan uwa, domin samun sulhu da karɓuwa.
“Shirin farfado da su ba zai yi tasiri ba idan ba a saka wadanda suka sha wahala ba. Dole a yi adalci ga kowa,” in ji shi.
Shugaban Sojin Kasa, Mejar Janar Waidi Shaibu, ya yi alkawarin murkushe kungiyar ta’addanci ta Lakurawa, wadda ke haddasa hare-hare a jihohin Arewa.
“Za mu murkushe ‘yan ta’addan Lakurawa gaba daya. Ba za su sake samun damar taruwa ko barazana ba,” in ji shi.
Shaibu ya kuma tunatar da kwarewarsa lokacin yakin Boko Haram a Borno a 2015, yana mai cewa zai ci gaba daga inda ya tsaya wajen tabbatar da tsaro.
Shugaban Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya bayyana aniyar sa na jagorantar rundunar sama mai horo, tsari, da ingantacciyar fasaha.
“Mutum da yake gudu daga gare ka ba zai iya shirya makirci a kanka ba,” in ji shi, yana mai jaddada bukatar tabbatar da mamayar sama ta hanyar bayanan leƙen asiri, hare-hare na kai tsaye, da shirin gaggawa.
Aneke ya bayyana cewa hangen nesansa yana kan horarwa, fasaha, tsaro, da kirkire-kirkire, yana mai cewa: “Karfin soji na gaskiya ba ya cikin karfi kawai, amma cikin dabaru da ilimin shugabanci.”
A ƙarshe, sabbin shugabannin tsaron sun yi alkawarin yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro ta hanyar dabaru masu dogaro da bayanan leƙen asiri da hadin kan al’umma. Sun kuma bukaci ƙarin kuɗaɗe da mayar da hankali kan samar da kayan tsaro a cikin gida domin rage dogaro da kasashen waje da kuma gina tsarin tsaro mai ɗorewa.



