Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa jami’an Hukumar Leken Asiri ta Tsaro (Defence Intelligence Agency – DIA) sun kai samame a gidan tsohon Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva, da ke Abuja, bisa zargin cewa yana da hannu a wani shirin juyin mulki. A yayin aikin, an ce sun kama dan uwansa mai suna Paga Sylva.
Majiyoyi sun bayyana cewa an kai samamen ne bayan samun bayanan sirri da suka danganta wasu ‘yan siyasa da zargin shirin tada zaune tsaye da nufin kawo cikas ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun ce Sylva, wanda ya taba zama Gwamnan Jihar Bayelsa, ya gudu daga Najeriya ta cikin kogunan yankin Neja Delta zuwa Senegal, inda ake zargin yana shirin wucewa zuwa ƙasar Argentina, inda yake da wasu harkokin kasuwanci.
Wani majiyar cikin gida ya bayyana cewa ɗaya daga cikin jami’an soja da aka fara kama da zargin hannu a shirin juyin mulkin ya ambaci sunan tsohon Ministan yayin bincike. Haka kuma, an ce masu bincike sun gano kusan naira biliyan 46 a wani asusun da ake zargin yana da alaka da shi.
Rahotanni sun kuma nuna cewa jami’an tsaro sun kai samame a gidan Sylva da ke Bayelsa, inda aka ce sun gano tarin kuɗaɗe a kudi na kasashen waje tare da wasu muhimman takardu da ake zargin suna da nasaba da binciken.
A gefe guda, wasu rahotanni sun ce iyalan Al-Makura sun nemi taimakon malamai bayan kama ɗansu, wani Laftanar Kanal da ke bakin aiki, wanda shi ma ake zargin yana da alaka da binciken.
Haka kuma, wasu majiyoyi sun bayyana cewa Sylva ya nuna fushi bayan sake nasarar Gwamna Douye Diri a Bayelsa, inda ya zargi jam’iyyarsa ta APC da rashin “yin abin da ya dace” domin tabbatar da nasararsa.
A halin yanzu, babu wata sanarwa daga Hedkwatar Tsaro ko daga Sylva kansa game da wannan zargi.



