Kungiyar Tsoffin Daliban Cibiyar Kasa ta Nazari kan Tsare Tsare da Dabarun Mulki (AANI) ta taya Lieutenant Janar Olufemi Olusola Oluyede murna bisa nadin sa da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin sabon Babban Hafsan Tsaro (Chief of Defence Staff) na Nijeriya.
A cikin sakon taya murnar da Shugaban kungiyar, Jakada Emmanuel Obi Okafor, ya sanya wa hannu, AANI ta bayyana wannan nadi a matsayin babban yabo da girmamawa ga kyakkyawar hidima, kwarewa, da bajintar shugabanci da Janar Oluyede ya nuna a harkokin soja da tsaro.
Jakada Okafor ya bayyana cewa wannan nadi shaida ce ta gaskiya kan nagartar halin Janar Oluyede, hankalinsa, da jarumtar sa, yana mai jaddada cewa nadin nasa alamar cikakken amincewar gwamnatin tarayya ne ga karfinsa wajen jagorantar dakarun sojojin Nijeriya domin fuskantar kalubalen tsaro da kasar ke ciki.
Ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa wannan mataki na hangen nesa da ke nuna fifikon cancanta, yana mai cewa wannan nadi ya kara nuna irin rawar da Cibiyar NIPSS ke takawa wajen samar da shugabanni masu hangen nesa da kuma kwarewar aiki wajen tsara manufofi.
Shugaban AANI ya kuma nuna godiya ga tsohon Babban Hafsan Tsaro da sauran hafsoshin rundunonin soji bisa gudunmawar da suka bayar wajen tsaron kasa da gina kasa, tare da yi musu fatan alheri da jagorancin Allah yayin da suke yin ritaya daga ayyukan soja.
Yayin da Lieutenant Janar Oluyede yake karbar sabbin nauyin sa a matsayin Babban Hafsan Tsaro, Okafor ya ce AANI na yi masa fatan nasara, hikima, karfi, da hadin kai domin ci gaba da samun nasara a yakin da ake yi da ta’addanci, ‘yan fashi da sauran barazanar tsaro da ke addabar kasa.
Ya tabbatar da cewa Kungiyar Tsoffin Daliban Cibiyar Kasa za ta ci gaba da goyon bayan sa da kuma hada kai da rundunonin sojojin Nijeriya domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da ci gaban kasa bisa taken su na Towards a better society wato Don ingantacciyar al’umma.




