Hukumar Kashe Gobara ta Babban Birnin Tarayya (FCT Fire Service) ta bayyana cewa ta ceci mutane 69 tare da kare dukiyoyi masu darajar Naira 14,466,915,000 daga gobara daban-daban da suka faru tsakanin watan Janairu zuwa Satumba, 2025.
Wannan bayani ya fito ne daga rahoton kididdigar kashe gobara da ceto da kakakin hukumar, Ibrahim Mohammad, ya fitar a ranar Laraba a birnin Abuja.
Mohammad ya bayyana cewa duk da gaggawar martani da nasarorin da aka samu wajen aikin ceto, an rasa rayuka 18 tare da dukiyoyin da suka kai darajar Naira 6,072,214,500 a lokacin. Ya ce wannan adadi na nuna yawaitar aukuwar gobara a yankin Babban Birnin Tarayya, tare da jaddada cewa hukumar na ci gaba da kokari wajen inganta matakan gaggawa da hana aukuwar gobara a cikin ƙananan hukumomi guda shida na FCT.
A cewar rahoton, hukumar ta gudanar da ayyukan ceto da dama a cikin wadannan watanni tara. Watan Maris ne ya fi yawan mutanen da aka ceci, inda aka kubutar da mutane 30, sai Yuni da mutane 22, Afirilu 13, da kuma Yuli 4. Babu asarar rai da aka samu a watannin Janairu, Fabrairu, Mayu, Agusta da Satumba.
Sai dai watannin Maris da Afirilu ne suka fi muni, inda aka rasa rayuka goma da takwas sakamakon gobara, yayin da sauran watanni suka wuce ba tare da asarar rai ba.
Rahoton ya kuma nuna cewa an karɓi kiran gobara guda 338 tsakanin watan Janairu da Satumba. Fabrairu ce ta fi da kira 64, sai Janairu da 59, Afirilu 51, Yuni 35, Maris 33, Mayu 31, Yuli 24, Agusta 21, da Satumba 20.
Haka kuma, hukumar ta amsa kiran ceto guda tara a cikin wannan lokaci, wanda ke nuna shirin ta na fuskantar kowace irin matsalar gaggawa ba wai ta gobara kawai ba.
Mohammad ya sake jaddada kudirin hukumar na rage asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon gobara ta hanyar wayar da kai ga jama’a, gaggawar martani, da kuma inganta haɗin gwiwa da sauran hukumomin gaggawa.
Ya kuma yi kira ga mazauna FCT da su kara kula da tsaro a gidajensu, wuraren aiki, da kasuwanni, musamman yayin da ake shirin shiga lokacin rani wanda yawanci ke da haɗarin gobara.
Kakakin hukumar ya ƙara da cewa Hukumar Kashe Gobara ta FCT na ƙara wayar da kai kan hanyoyin kare kai daga gobara, amfani da kayan lantarki yadda ya dace, da bin ka’idojin tsaro a gidaje da wuraren kasuwanci domin kauce wa hadarurruka da za a iya guje musu.




