Shugaban Tsaron Kasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa, ya yaba wa Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa bisa jajircewar su wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da kwanciyar hankali a kasa baki ɗaya.
Ya bayyana hakan ne a cikin sakon gaisuwa da ya gabatar a yayin babban taron Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa da aka gudanar a ranar Talata, 21 ga Oktoba, 2025 a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi.
Janar Musa ya taya mai girma Sarkin Musulmi, shugaban majalisar, da sauran manyan sarakuna murna, inda ya bayyana taken taron mai cewa “Ƙarfafa Hadin Gwiwar Al’umma Domin Samun Zaman Lafiya da Tsaro Mai Dorewa a Arewacin Najeriya,” a matsayin abin da ya dace kuma mai muhimmanci. Ya jaddada cewa sarakunan gargajiya su ne ginshiƙan al’adu, tarbiyya da hadin kan jama’a — muhimman abubuwa da ke tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Janar Musa ya bayyana cewa sarakunan gargajiya su ne tubalin mulki kuma su ne matakin farko da gwamnati ke hulɗa da jama’a. Ya yabawa rawar da suke takawa wajen sasanta rikice-rikice, zaman sulhu da tattara bayanan sirri, yana mai cewa goyon bayan su ya taimaka sosai wajen nasarar rundunonin sojoji a wuraren da ake gudanar da ayyukan tsaro.
Ya kara da cewa zaman lafiya da tsaro ba za a tilasta su ba, sai ta hanyar amincewa, tattaunawa da hadin kai tsakanin al’umma. Saboda haka, ya yi kira da a rungumi tsarin haɗin kai na “dukkan al’umma,” wanda ya haɗa da sarakunan gargajiya, matasa, kungiyoyin mata, shugabannin addinai da hukumomin gwamnati domin yakar tashin hankali da wanzar da hadin kai da juriya.
Janar Musa ya tabbatar wa majalisar cewa rundunar sojojin Najeriya za ta ci gaba da kare yankin kasar da rayuwar ‘yan kasa, tare da nuna godiya bisa goyon bayan da suke samu daga sarakunan gargajiya. Ya yi kira da a ci gaba da wannan haɗin kai domin samun zaman lafiya mai dorewa a Arewacin Najeriya da kasa baki ɗaya.
Ya kuma yaba wa Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa bisa hangen nesa da jajircewar su wajen ci gaban yankin, yana fatan taron zai ƙara ƙarfafa haɗin kai da sabunta fata kan samun zaman lafiya da haɗin kan al’umma.
Tun da farko, a lokacin da ya kai ziyara gidan gwamnatin Jihar Kebbi, Janar Musa ya yabawa ci gaban da gwamnatin jihar ke samu tare da nuna farin ciki da kasancewarsa a Kebbi, wanda ya bayyana a matsayin “gida.” Ya gode wa Gwamna bisa goyon bayan da yake baiwa rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro, yana mai cewa irin wannan haɗin kai yana da matuƙar muhimmanci wajen nasarar ayyukan tsaro.
A martaninsa, Gwamnan Jihar Kebbi ya yaba da ƙoƙarin sojoji wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar. Ya ce wannan jajircewa ta cancanci dukkan goyon baya, wanda ya sa gwamnati ta raba motocin aiki da kayan aiki ga hukumomin tsaro. Gwamnan ya kuma gode wa CDS bisa tura motocin yaki da dakarun musamman domin ƙarfafa yaki da rashin tsaro a yankin, yana bayyana salon jagorancin Janar Musa a matsayin abin koyi da kwarin gwiwa.
A wani bangare, CDS zai halarci wasan ƙarshe na Kofin Zaman Lafiya da Haɗin Kai na Janar Christopher Musa 2025 da za a gudanar a filin wasa na FIFA Goal Project, Birnin Kebbi. Gasar ƙwallon ƙafar na da nufin ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da zumunci tsakanin jama’a, inda ta haɗa mahalarta daga jihohin Kebbi, Sokoto da Zamfara. Ana kuma sa ran Gwamnan Jihar Kebbi zai halarci wasan ƙarshe.




