Hedkwatar Hukumar Tsaro da Kare Jama’a (NSCDC) reshen Jihar Lagos ta sake jaddada kudurinta na kare muhimman gine-ginen gwamnati, musamman gadar 3rd Mainland, Carter da Eko, tare da daukar matakai na musamman don hana ayyukan hakar ma’adinai da guna ba tare da izini ba a fadin jihar.
Wannan kuduri ya samu karfi ne a yayin taron tattaunawar masu ruwa da tsaki karo na biyu da aka gudanar a yau Laraba, 22 ga Oktoba, 2025, a harabar Federal Secretariat, TBS, Obalende, Lagos. Taron ya samu halartar manyan wakilai daga hukumomi daban-daban na gwamnati da masu ruwa da tsaki daga bangarori masu muhimmanci.
Cikin wadanda suka halarta akwai wakilai daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, Ma’aikatar Ma’adinai da Karafa ta Tarayya, Ofishin Surveyor-General Liaison Office, Ma’aikatar Makamashi da Albarkatun Ma’adinai ta Jihar Lagos, Hukumar Ruwa ta Kasa (NIWA), da Hukumar Ruwa ta Jihar Lagos (LASWA), da sauransu.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Bimbola Salu-Hundeyin, ta yaba wa NSCDC bisa jagorancin wannan muhimmin shiri, tana mai cewa manufar ta dace da tsarin THEMES na Gwamna Babajide Olusola Sanwo-Olu, wanda ke mai da hankali kan ci gaban dorewa da ingantaccen rayuwa ga ‘yan Lagos.
Ta jaddada bukatar hadin kai tsakanin dukkan hukumomin da abin ya shafa don tabbatar da tsaron da dorewar gadar 3rd Mainland, Carter da Eko, tana mai cewa Gwamnatin Jihar ta kuduri aniyar samar da yanayi mai aminci da dorewa ga al’ummar Lagos.
A nasa jawabin, Kwamandan NSCDC na Jihar Lagos, Mista Keshinro Adedotun, ya bayyana cewa kokarin da suke yi na bin umarnin Ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Kasa (ONSA) ne, tare da nufin karfafa hadin kai tsakanin hukumomi wajen dakile barazanar da ayyukan hakar ma’adinai da guna ba bisa ka’ida ba ke haifarwa.
Kwamandan ya kuma bayyana bukatar kafa kwamitin hadin gwiwa domin gudanar da binciken gaggawa a wuraren da ake guna da hakar ma’adinai, tare da hadawa da al’ummomin yankuna don tabbatar da sahihin bayanai da rahotanni.
An kammala taron da yarjejeniya daga dukkan mahalarta cewa a kafa kwamitin aiki nan take domin fara duba wuraren guna da hakar ma’adinai, sannan a fara cikakken aiwatar da matakan tilastawa bayan kammala taron yau.





