Ƙungiyar Daliban Jihar Kogi ta Ƙasa (NAKOSS), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta na Ƙasa, Mr. Sunday Adeola Simon, ta kai ziyarar ban girma ga Babban Kwamandan Hukumar Kula da Wuta ta Ƙasa (FFS), Olumode Samuel Adeyemi, FCNA, ACTI, a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
Manufar ziyarar ita ce naɗa Babban Kwamandan a matsayin Babban Mai Tallafawa (Grand Patron), domin girmama irin jajircewarsa, ƙwarewarsa a shugabanci, da sadaukar da kai wajen kare rayuka da dukiyar jama’a. Haka kuma, ziyarar ta zama dama ga ƙungiyar don bayyana cikakken goyon bayanta ga Hukumar Kula da Wuta da kuma ƙudurin ta na yaɗa ilimin tsaro daga gobara a cikin makarantun gaba da sakandare a Jihar Kogi da sauran wurare.
A yayin ziyarar, tawagar NAKOSS ta mika kyaftin girmamawa ga Babban Kwamandan domin nuna yabo da godiya bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen gina ƙasa da kuma kyakkyawan jagoranci a harkokin gwamnati.
A cikin jawabinsa, Babban Kwamandan Adeyemi ya nuna matuƙar farin ciki da godiya ga ƙungiyar bisa wannan karramawa. Ya yaba da ƙwazon daliban wajen ɗaukar matakai masu amfani ga al’umma, tare da ƙarfafa su da su ci gaba da zama jakadu nagari na Jihar Kogi, musamman a matsayin jakadu na tsaro daga gobara a cikin jami’o’i da kwalejojin su.
Ya jaddada cewa ilimin tsaro daga gobara dole ne ya zama wani ɓangare na rayuwar kowanne ɗalibi, domin sanin hanyoyin kariya da amsa gaggawa na iya ceton rayuka da dukiyar jama’a.
Babban Kwamandan ya kuma tabbatar wa ƙungiyar NAKOSS da cewa Hukumar Kula da Wuta za ta ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ɗalibai wajen gudanar da wayar da kai kan gobara, kafa kulake na tsaro, da shirya horaswa da ƙarfafa ƙwarewa a jami’o’i da kwalejoji a faɗin ƙasar nan.





