Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Muhimman Abubuwa ta Kasa (NSCDC) reshen Jihar Sokoto, Kwamanda Emmanuel Adesina Ajayi (CC E.A. Ajayi), ya shawarci mahalarta taron horo na kwanaki biyu da su yi amfani da wannan dama domin inganta kwarewarsu da kuma ingancin aikinsu wajen gudanar da ayyuka.
An shirya horon ne tare da hadin gwiwar Kamfanin Galaxy Digital World Limited, domin fadada tunanin mahalarta, karfafa sanin kai, da kuma kara fahimtar rawar da suke takawa wajen tabbatar da ingantaccen aiki da bayar da hidima mai inganci ga jama’a.
Kwamanda Ajayi ya bayyana cewa wannan shirin na da nasaba da hangen nesan Kwamandan Janar na NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, mni, OFR, wanda ya sadaukar da kai wajen sake fasalin hukumar domin karfafa sana’a, ladabi, da ingantacciyar ayyuka a matakai daban-daban.
Ya jaddada cewa ci gaba da horaswa da sake horas da jami’ai shi ne ginshikin cimma babban manufa ta kare rayuka da dukiyoyi, inda ya kara da cewa horon zai baiwa mahalarta damar koyon sabbin dabaru na shugabanci, samar da aiki mai inganci, da gudanar da ayyuka a fagen aiki cikin kwarewa.
An gudanar da shirin mai taken “Inganta Ayyukan Hidima”, wanda ya mayar da hankali kan batutuwa kamar Basira ta Wandaké (Artificial Intelligence) da Gudanar da Shari’u (Case Handling), domin baiwa jami’an NSCDC sabbin dabaru na zamani don inganta aiki da samar da sakamako mai kyau.




