Kwamandan Brigade ta 3 na Rundunar Sojin Najeriya, Brigediya Janar Ahmed Tukur, ya tabbatar da kudurin rundunar wajen ci gaba da hadin kai tsakanin hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Jihar Kano.
Brigediya Janar Tukur ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 17 ga Oktoba, 2025, lokacin da ya karbi bakuncin Kwamandan Hukumar Tsaro ta Farar Hula (NSCDC), Jihar Kano, Mista Bala Bawa Bodinga, da Kwamandan Kwalejin Horar da Ma’aikatan Kwastam, Mataimakin Kwampta Umar Atiku, yayin ziyarar ban girma da suka kai hedkwatar Brigade din a Kano.
Janar Tukur ya jaddada cewa hadin kai tsakanin hukumomin tsaro yana da matukar muhimmanci wajen musayar bayanan sirri, daidaituwa, da gaggawar daukar mataki kan sabbin barazanar tsaro. Ya ce, “Ina matukar farin cikin karbar Kwamandan NSCDC da tawagarsa a yau. Na gamsu da yadda kuka fara aiki da sauri ta hanyar neman hadin kai da sauran hukumomin tsaro a jihar, wanda hakan ke kara karfafa zumunci da fahimtar juna.”
Ya kara da cewa Rundunar Sojin Najeriya za ta ci gaba da tabbatar da shirin ta na aiki don tabbatar da cewa jihar Kano ta ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da yanayin da kasuwanci da harkokin rayuwa za su bunkasa. Janar din ya kuma tabbatar wa Kwamandan NSCDC da Kwamandan Kwalejin Kwastam cewa rundunar za ta ci gaba da bayar da duk wata goyon baya da ake bukata a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
A nasa bangaren, Kwamandan NSCDC, Mista Bala Bawa Bodinga, ya gode wa Brigade din bisa kyakkyawar tarba da kulawa, tare da tabbatar da aniyar hukumar wajen ci gaba da




