Hukumar People’s Security Monitor (PSM) na farin cikin sanar da cewa za a gudanar da Taron Tsaro na Shekara ta 2025 tare da Lambar Girmamawa ta People’s Security Monitor a ranar Laraba, 10 ga Disamba, 2025, a Nigerian National Merit Award House, Maitama, Abuja.
Wannan gagarumin taron zai kasance dandali na tattaunawa da nazari kan halin da ake ciki a fannin tsaro a Najeriya, inda masana tsaro, masu tsara manufofi da sauran kwararru za su hadu domin tattaunawa da gabatar da hanyoyin da za su kara karfafa tsaro da dorewar zaman lafiya a kasa.
Baya ga tattaunawa mai ma’ana, za a kuma karrama ‘yan Najeriya nagari a bangaren tsaro — wadanda suka nuna sadaukarwa, gaskiya, da kwararru wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Bugu da kari, wannan bugu na shekarar 2025 yana dauke da jerin jawabai na manyan baki, tattaunawa ta kwamiti, da kuma bayar da lambobin yabo ga mutanen da suka yi fice a harkokin tsaro da jin kai.
Domin karin bayani ko halarta, a tuntubi sakatariyar taron ta:
📞 +234 (0) 805 500 1816
📧 info@pressgallery2013@gmail.com




