Kungiyar Injiniyoyin Na’ura ta Najeriya (NIMechE) ta gudanar da taronta na kasa da kasa karo na 38 tare da babban taron shekara a ranar Alhamis, 17 ga Oktoba, 2025, a Ikeja, Legas.
Taron ya tattaro kwararru, masana da shugabanni daga fannoni daban-daban don yin bikin girmamawa ga hazaka, ci gaban sana’a, da kuma bajintar da ke nuna kwarewa a fannin injiniyanci.
Shugaban Hukumar Tsaro ta Jama’a da Kare Muhalli (NSCDC), Farfesa Ahmed Abubakar Audi, ya samu wakilci daga kwamandan jihar Legas, Mista Keshinro Adedotun, wanda ya halarci taron domin girmama daya daga cikin jami’an hukumar, Commandant of Corps Onanuga Idowu Afolabi, MNSE, MNIMechE, wanda aka karrama da matsayin Fellow na kungiyar.
Farfesa Audi ya jaddada kudurinsa na ci gaba da baiwa jami’an NSCDC damar samun karin horo da cigaban sana’a a cikin gida da waje, domin kara musu kwarewa da inganta ayyukan su na kare rayuka da dukiyoyin kasa.




