Hukumar Kula da Wuta ta Ƙasa, Sashen Jihar Rivers, ta gudanar da bikin mika mulki a ranar Laraba, 15 ga Oktoba, 2025, inda tsohuwar Kontrola ta Jiha, ACF Hawa Weli, ta mika ragamar mulki ga sabon da aka nada, ACF Obasi Ikenna.
An gudanar da wannan muhimmiyar bukin a Hedikwatar Hukumar da ke Port Harcourt, wanda ke nuna sauyin shugabanci cikin lumana da nufin tabbatar da ci gaba da ingantaccen aiki da kuma ƙarfafa jajircewar Hukumar wajen kare rayuka da dukiyoyi daga gobara a faɗin jihar.
A cikin jawabin bankwana, ACF Hawa Weli ta gode wa shugabanci da jami’an hukumar bisa goyon baya da hadin kai da suka nuna a lokacin aikinta, tare da kira gare su da su ci gaba da nuna irin wannan kishin da haɗin kai ga sabon Kontrola.
Shi kuwa sabon Kontrola na Jiha, ACF Obasi Ikenna, a jawabinsa na farko, ya gode wa Babban Kontrola Janar na Hukumar, Dakta Olumide Samuel Adeyemi, bisa amincewar da ya nuna gare shi da kuma damar da aka ba shi na yi wa ƙasa hidima. Ya yi alkawarin gina kan nasarorin da wanda ya gabace shi ya samu tare da ƙara ƙarfafa hanyoyin rigakafi da martani cikin gaggawa ga matsalolin gobara a Jihar Rivers.
An halarci bukin mika mulkin ne da jami’ai da ma’aikatan Hukumar, waɗanda suka bayyana shirinsu na mara baya ga sabon shugabanci domin cika manufofin Hukumar.




