Kwamandan Janar na Hukumar Tsaro ta Jama’a da Kare Muhimman Ababen Gini (NSCDC), Farfesa Ahmed Abubakar Audi, ya yi godiya tare da girmamawa ga marigayi Kwamandan Jihar Edo, Kwamandan Corps Agun Gbenga, inda ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen jami’i mai himma da sadaukarwa, wanda ayyukansa da kyakkyawan gadonsa za su ci gaba da zama abin koyi ga sauran jami’an hukumar.
A ranar Alhamis, 16 ga Oktoba, 2025, Kwamandan Janar ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin ta hannun wata tawaga ta musamman daga Hedikwatar NSCDC dake Abuja. Tawagar ta samu jagorancin Mataimakin Kwamandan Janar (DCG) Adeyinka Fasiu Ayinla, wanda ke jagorantar Daraktar Kula da Harkokin Gudanarwa (Directorate of Administration). Tawagar ta ziyarci gidan marigayin da ke Meran, Agbado, a yankin Oke-Odo Local Council Development Area, Jihar Legas.
A cikin saƙonsa, Farfesa Audi ya bayyana tausayin hukumar ga iyalan marigayin tare da yaba wa gudunmawar da marigayin ya bayar wajen bunƙasa hukumar NSCDC da tsarin tsaro gaba ɗaya a ƙasar. Ya yi addu’ar Allah Ya jikansa, Ya ba shi hutu na har abada, tare da bai wa iyalan marigayin ƙarfin hali da natsuwa a wannan lokacin na jimami.
Iyalan marigayin sun tarbi tawagar NSCDC da farin ciki tare da bayyana godiya ga Kwamandan Janar bisa kulawa da goyon bayansa. A madadin Kwamandan Janar, DCG Ayinla ya sanya hannu a kundin ta’aziyya domin girmama marigayin, a matsayin alamar tunawa da girmamawa.




