Kwamandan Hukumar Tsaro ta Jama’a da Kare Muhimman Ababen Gini (NSCDC) na Jihar Kano, Kwamanda Bala Bawa Bodinga, ya sake jaddada kudirin hukumar na ƙarfafa haɗin kai da rundunar sojojin ƙasa, rundunar sojin sama, da sauran hukumomin tsaro da abokan hulɗa a jihar.
A ci gaba da ziyarar ban girma da yake kaiwa hukumomin tsaro da abokan hulɗa a Kano, Kwamanda Bodinga ya kai ziyara ga Brigade ta 3 ta rundunar sojojin ƙasa dake Bukavu Barracks, Kano, da kuma 455 Base Services Group na rundunar sojin sama.
Yayin ziyarar, Kwamanda Bodinga ya jaddada muhimmancin haɗin kai, fahimtar juna, da ci gaba da tattaunawa tsakanin hukumomin tsaro domin shawo kan barazanar da ke ƙalubalantar zaman lafiya da tsaro. Ya yaba da kyakkyawar dangantaka da ke tsakanin hukumomin tsaro a jihar Kano, inda ya sha alwashin ƙara ƙarfafa wannan haɗin kai domin amfanin al’umma gaba ɗaya.
“Na shaida da idona irin kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin hukumomin tsaro a Kano. Na kuduri aniyar ƙara ƙarfafa wannan haɗin kai domin ’yan ƙasa su ci gaba da kwanciyar hankali ba tare da tsoro ba,” in ji Kwamanda Bodinga.
A hedkwatar Brigade ta 3, Kwamandan Brigade ɗin, Birgediya Janar Ahmed Muhammad Tukur, ya tarbi tawagar NSCDC da farin ciki, inda ya bayyana cewa zuwan Kwamanda Bodinga Kano wata babbar dama ce ga tsarin tsaro na jihar. Ya bayyana tabbacin cewa haɗin gwiwar da ke tsakanin sojoji da hukumar NSCDC zai taimaka matuƙa wajen magance matsalolin tsaro.
Haka zalika, a 455 Base Services Group, Kwamandan Base ɗin, Group Captain Mustapha Suleiman, ya yaba da NSCDC bisa ƙa’idarta ta ladabi, biyayya, da ƙwarewa. Ya kuma gode wa Kwamandan Janar na NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, mni, OFR, bisa nadin Kwamanda Bodinga a matsayin kwamandan jihar Kano, yana mai cewa ƙwarewarsa da kwarewar jagoranci za su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro a jihar. Ya kuma yi alkawarin ci gaba da goyon baya ga hukumar, musamman wajen kare muhimman ababen more rayuwa na ƙasa.
A wani ɓangare na wannan ci gaba, Kwamanda Bodinga ya kai ziyarar ban girma ga kamfanin jiragen sama na Max Air Limited, Kano, inda Mataimakin Shugaban Kamfanin, Alhaji Abubakar Dahiru Mangal, ya tarbe shi da farin ciki. Bangarorin biyu sun amince da sabunta da kuma ƙarfafa dangantakar haɗin gwiwa mai amfani ga juna.




