Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Jama’a ta Ƙasa (NSCDC) na Babban Birnin Tarayya, Dokta Olusola Odumosu, ya bukaci a ƙarfafa tsarin inshorar rayuwa da lafiya ga jami’an hukumar, yana mai jaddada cewa jami’an suna fuskantar haɗurra da matsaloli a kullum yayin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Odumosu ya yi wannan kira ne a ranar Juma’a yayin taron wayar da kai na yini guda kan muhimmancin inshora da aka gudanar a hedkwatar hukumar da ke Wuse Zone 5, Abuja.
Ya bayyana cewa inshora muhimmin sashi ne na jin daɗin ma’aikata, musamman ganin yadda aikin NSCDC ke cike da haɗari — ciki har da magance tarzoma, yaƙi da ‘yan ta’adda, da kuma fatattakar masu fasa bututun mai.
“Inshora tana da matuƙar muhimmanci ga jami’anmu saboda irin haɗarin da suke fuskanta a kowane lokaci yayin aiwatar da aikinsu,” in ji Odumosu.
Ya ce, kasancewar NSCDC hukuma ce ta paramilitary, wajibi ne ta ci gaba da wayar da kan jami’anta game da nau’o’in inshorar da gwamnati ta samar, irin su inshorar rai, haɗari, da ta wurin aiki, da kuma tsare-tsaren da ke haɗa tanadi da fansho bayan yin ritaya.
“Gwamnati, a matsayin wajibinta na doka da ɗabi’a, ta samar da manufofi don kare waɗanda ke kare al’umma ta hanyar samar da ingantaccen tsarin inshora a matsayin muhimmin ɓangare na walwala da haƙƙin ɗan adam,” in ji shi.
Odumosu ya ƙara da cewa inshora tana ba da kariya ta kuɗi ga jami’an da suka samu rauni, nakasa, ko suka rasu yayin aiki, domin tabbatar da cewa iyalansu ba su shiga cikin wahala ba.
Ya yaba wa Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, bisa jajircewarsa wajen inganta jin daɗin ma’aikata ta hanyar samar da tsare-tsaren inshora daban-daban a faɗin ƙasar.
“Babban Kwamanda ya nuna hazaka ta musamman wajen tabbatar da cewa iyalan jarumai da suka rasu ko waɗanda suka ji rauni suna karɓar takardun biyan kuɗi masu darajar miliyoyin naira,” in ji Odumosu.
Ya ƙara da yabawa CG bisa tabbatar da biyan fa’idar inshora cikin lokaci, wanda ya ƙara wa jami’ai ƙwarin gwiwa a faɗin ƙasar.
Kwamandan FCT ɗin ya kuma umarci shugabannin sassa, kwamandojin yankuna, da jami’an rassa su yada ilimin da suka samu daga taron ga ƙananan jami’ai, don tabbatar da cewa kowa ya amfana da manufofin walwala na gwamnati.
Odumosu ya kuma roƙi kamfanonin inshora da su nuna gaskiya da amana a hulɗarsu da hukumomin tsaro, tare da kawar da matsalolin burokrasiya da ke jinkirta biyan fa’idodin inshora.
“Na roƙi kamfanonin inshora da su sauƙaƙa tsarin su, tare da ba jami’ai bayanai masu inganci domin su iya yanke shawarar da ta dace,” in ji shi a ƙarshe.
Taron ya tattaro manyan jami’ai, kwamandojin yankuna, jami’an rassa da shugabannin sassa daga dukkanin ɓangarorin hukumar a Babban Birnin Tarayya.




