Kwamandan SouthWest Security Network (Amotekun Corps) na Jihar Ondo, Akogun Adetunji Adeleye, ya yi girmamawa ga marigayi SC Oluwole Oludare Emmanuel, jami’in NSCDC na Jihar Ondo, wanda ya rasu ‘yan makonni da suka gabata.
Marigayi SC Oluwole Oludare ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya. Shi ne jami’in da ke kula da Joint Task Force (JTF) da gwamnatin jihar ta kafa don tsare lafiyar jama’a a yankin Akure North.
Yayin ziyarar ta’aziyya zuwa hedikwatar hukumar, Akogun Adeleye ya tabbatar wa iyalan marigayin da ci gaba da tallafi daga hukumar, tare da mika musu kyautar yabo don nuna godiya bisa jarumta da sadaukarwar da marigayin ya yi a bakin aiki.
Kwamandan NSCDC na Jihar Ondo, CC Oluyemi Ibiloye, ya gode wa Kwamandan Amotekun bisa wannan karamci, tare da tabbatar da cewa hukumar NSCDC za ta ci gaba da haɗin kai da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron jihar Ondo.
Dukkan shugabannin tsaron sun kuma yi alkawarin duba damar aikin gwamnati ga ɗan marigayin wanda ya nuna sha’awar shiga cikin ɗaya daga cikin hukumomin tsaro.
Ziyarar ta’aziyyar ta samu halartar iyalan marigayin, manyan jami’an NSCDC, da kuma mambobin rundunar Amotekun.





