A ci gaba da ziyarar aikinsa zuwa cibiyoyin Hukumar Kariya Daga Gobara ta Tarayya (Federal Fire Service – FFS) da ke cikin Babban Birnin Tarayya, Kwamandan Janar na Hukumar, Dakta Olumode Samuel Adeyemi, FCNA, ACTI, ya kai ziyarar duba aiki zuwa cibiyoyin Nyanya da Apo a yau, Talata, 14 ga Oktoba, 2025, tare da manyan jami’an gudanarwa na hukumar.
Ma’aikata daga sassa daban-daban na Ma’aikatun Gwamnati (MDAs) suma sun halarci zaman tattaunawa da aka gudanar, inda aka tattauna kan matsalolin aiki da hanyoyin inganta ayyuka.
A yayin ziyarar, Kwamandan Janar ya zagaya wuraren aiki, ya duba kayan aiki da yanayin su, sannan ya saurari koke-koke da matsalolin da jami’ai da ma’aikata na cibiyoyin suka gabatar masa, musamman kan walwala, kayan aiki, da ingancin ayyuka.
A jawabinsa, Dakta Olumode ya tabbatar da kudirin hukumarsa na ci gaba da inganta walwalar ma’aikata, magance gibin aiki, da kuma samar da goyon bayan da ake bukata domin tabbatar da ingantaccen gudanar da aiki. Ya yaba wa jami’an bisa jajircewa da kwarewar su, yana kuma karfafa musu gwiwa da su ci gaba da kasancewa masu ladabi, tsari, da kwazo a yayin gudanar da aikinsu.
Wannan ziyara ta kara nuna irin jagorancin kai tsaye da Kwamandan Janar ke yi, tare da nuni da aniyarsa na tabbatar da cewa dukkan cibiyoyin Hukumar Kariya Daga Gobara a fadin kasar suna da kayan aiki da kwarin gwiwar da ake bukata domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma yadda ya kamata.





