Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Ƙasa (NSCDC) na Jihar Legas, Mista Keshinro Adedotun, ya karrama jami’ai goma (10) da suka nuna bajinta a cikin horo da sake horarwa da aka gudanar a Kwalejin Kula da Tsaro da ke Oke-Mosan, Abeokuta, Jihar Ogun.
An gudanar da bikin karramawar ne yayin taron muster parade da aka shirya a Hedikwatar Hukumar da ke Alausa, Ikeja, a ranar Talata, 14 ga Oktoba, 2025, inda Kwamandan ya karɓi sabbin jami’an da aka horar da kuma sake horarwa, guda dari biyu da saba’in da huɗu (274). Jami’an sun halarci shirye-shiryen ƙwarewa na COCATRAP, FOAHT, da Agro Rangers da aka gudanar tsakanin watan Mayu zuwa Oktoba, 2025, ga rukuni na A, B, da C.
Yayin da yake jawabi, Kwamandan Adedotun ya yaba wa jajircewa da himmar jami’an a lokacin horon, yana mai kira gare su da su ci gaba da aiki cikin kwarewa, gaskiya da bin ƙa’ida. Ya tunatar da su cewa halayensu da yadda suke gudanar da aiki na wakiltar martabar hukumar, don haka ya shawarce su da su kasance jakadu nagari na NSCDC a duk inda suke aiki.
A matsayin lada da yabo, Kwamandan ya ba wa jami’ai goma (10) da suka fi kowa fice a lokacin horo kyautar kuɗi, yana mai bayyana nasararsu a matsayin sakamakon jajircewa, daidaito da sadaukarwa.
Ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da mayar da hankali kan inganta ƙwarewa da horar da jami’anta, yana mai jaddada cewa ci gaba da horo da sake horarwa na da matuƙar muhimmanci wajen ƙara ingancin aiki da tabbatar da tsaron ƙasa.




