Babban Kwamandan Hukumar Kiyaye Gobara ta Ƙasa (FFS), CGF Olumode Adeyemi Samuel, ya nuna godiyarsa ta musamman ga Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Ƙasa (NSCDC) bisa jajircewarta wajen kare muhimman ababen more rayuwa a ƙasa da kuma samar da tsaro ga jami’an hukumar yayin ayyukan kashe gobara.
A yayin ziyarar ban girma da ya kai ga Babban Kwamandan NSCDC, Prof. Ahmed Abubakar Audi, a Hedikwatar Rundunar a Abuja, CGF ya yaba wa NSCDC bisa rawar da take takawa wajen tabbatar da tsaron motocin kashe gobara, jami’ai, da sauran ayyukan gaggawa yayin yanayi na hatsari.
Ya jaddada muhimmancin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin biyu, yana mai kira ga zurfafa haɗin kai, shirye-shiryen horo na haɗin gwiwa, da kuma daidaita dabarun aiki domin inganta amsa gaggawa a ƙasa. CGF Olumode ya kuma nemi ci gaba da bayar da tallafin tsaro ga ma’aikatan kashe gobara da kayan aiki, tare da gudanar da horo na haɗin gwiwa kan tsaro da daidaiton aiki a fili.
Yayin da yake yabon yadda NSCDC ke kula da tsaro a cikin cibiyoyinta, CGF ya nuna gamsuwa da yadda take gudanar da tsarin kiyaye wuta a cikin ofisoshi, inda ya bayyana hakan a matsayin kyakkyawan misali na shiri da kariya ga dukiya. Haka kuma ya bayyana cewa Hukumar Kiyaye Gobara ta Shirya yin amfani da ƙwarewar NSCDC da tsare-tsaren shugabanci domin cimma burin hukumomin biyu.
A martaninsa, Dr. Ahmed Abubakar Audi ya karɓi CGF da tawagarsa da hannu biyu, inda ya taya shi murna kan nadinsa. Ya bayyana matsayin shugabanci a matsayin amanar Allah, yana mai cewa “shugabanci na wucin gadi ne, kuma iko ba na dindindin bane.” Ya shawarci CGF da ya daidaita tsakanin “bukata da son zuciya,” ya fifita jin daɗin ma’aikata, kuma ya jagoranci da tawali’u da hikima.
Dr. Audi ya kuma yaba wa Hukumar Kiyaye Gobara bisa ƙarfafa haɗa ma’aikata mata a cikin ayyukan hukumar, inda ya bayyana hakan a matsayin mataki mai kyau na inganta daidaito a aikin gwamnati. Ya tabbatar wa CGF da cewa NSCDC za ta ci gaba da haɗin kai da bayar da tallafin tsaro ga ayyukan kashe gobara a duk faɗin ƙasa.
Babban Kwamandan NSCDC ya sake jaddada kudurinsa na ƙarfafa haɗin gwiwa da Hukumar Kiyaye Gobara ta Ƙasa ƙarƙashin “Ka’idar 3C” – Haɗin Kai, Haɗin Gwiwa da Ƙulla Dangantaka, a matsayin tsarin cimma ingantaccen tsaro da kyakkyawan gudanarwar ayyuka a ƙasa.




