Rundunar Yan Sandan Babban Birnin Tarayya FCT ta kama mutane 12 da ake zargi da aikata fashi da makami wanda ya yi sanadin mutuwar ma’aikaciyar tashar Arise News, Somtochukwu Christella Maduagwu, da mai gadin gidanta, Barnabas Danlami, a yayin wani harin fashi da aka kai a Abuja.
An kama wadanda ake zargin ne bayan wani gagarumin samame da rundunar Scorpion Squad ta gudanar a karkashin jagorancin ACP Victor Godfrey, bisa bayanan sirri da kamfanin Giga Forensics, reshen EIB STRATOC, ya bayar.
Rahotanni sun nuna cewa Kwamishinan Yan Sanda na FCT ya umarci a gudanar da bincike na musamman bayan harin da aka kai ranar 29 ga Satumba, 2025, a Unique Apartment, unguwar Gishiri, Katampe District, da misalin karfe 3:30 na safe.
Bayan samun sahihan bayanai, jami’an tsaro sun kama wadanda ake zargi da sunayen Shamsudeen Hassan, Hassan Isah, Abubakar Alkamu wanda aka fi sani da Abba, Sani Sirajo Dan Borume, Mashkur Jamilu, Suleiman Badamasi Dan Sule, Abdul Salam Saleh, Zaharadeen Muhammad, Musa Adamu, Sumayya Mohammed, Isah Abdulrahman, da Musa Umar.
An bayyana cewa an fara kama mutane hudu daga cikin su ne ta hanyar bibiyar wayoyin hannu da aka sace daga wajen mutanen da aka kai wa harin.
A lokacin tambayarsu, Hassan ya amsa cewa shi ne ya harbi mai gadin gidan, yayin da Sirajo ya ce ya yi kokarin hana Maduagwu faduwa daga saman bene lokacin rikicin.
Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da bindigar AK 47 ta gida, harsasai guda 36, bindiga kirar gida, bindigar pump action, harsasai biyu, wayoyi hudu mallakar wadanda abin ya rutsa da su, wuka, adda, da fitilun hannu tara.
Sauran mambobin kungiyar sun shiga hannun jami’an tsaro a ranar Laraba yayin da ake zargin suna kan hanyarsu ta kai wani sabon hari a yankin Maitama, Abuja.
Duk wadanda aka kama sun amsa laifin da ake zargin su da shi, kuma bincike yana ci gaba.
Maduagwu, wacce take aiki a matsayin mai gabatar da shirye-shirye da kuma mai tace labarai a Arise News, ta rasa ranta ne yayin harin fashi. Rahoton yan sanda ya tabbatar da cewa ta fadi daga bene na uku na gidanta yayin kokarin tserewa daga masu fashin, sabanin rahotannin farko da suka ce an harbe ta.
Mai gadin gidan Barnabas Danlami shima ya mutu yayin kokarin kare mazauna gidan daga masu harin.
Rundunar Yan Sandan FCT ta tabbatar wa jama’a cewa za a gurfanar da dukkan wadanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike, tare da ci gaba da neman sauran abokan harkarsu da ke tsere.




