Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Jama’a (NSCDC) na Jihar Legas, Kwamanda Keshinro Adedotun, a ranar Laraba, 8 ga Oktoba, 2025, ya jagoranci wata tawaga ta manyan jami’ai na hukumar zuwa gidan marigayi Kwamandan Jihar Edo, Kwamanda Agun Gbenga, domin yin ziyarar ta’aziyya. Ziyarar ta gudana ne a gidan marigayin da ke Meran, Agbado Oke-Odo, a karamar hukumar cigaban yankin Legas.
Yayin da yake jaje ga matar da ’ya’yan marigayi Kwamanda, Kwamanda Adedotun ya bayyana cewa ziyarar ta kasance ne bisa umarni da jagorancin Babban Kwamandan NSCDC na kasa, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, wanda ya nuna matukar jimami da alhini kan rasuwar daya daga cikin kwararrun jami’ai masu kishin aiki a hukumar.
Ya kuma bayyana cewa wata tawaga ta musamman daga Babban Hedikwatar NSCDC da ke Abuja za ta kai irin wannan ziyara nan ba da jimawa ba domin mika sakon ta’aziyyar hukumar ga iyalin marigayin ta hanyar hukuma.
A cikin jawabinsa, wanda ya wakilci iyalin marigayi Kwamanda, ya mika godiya ta musamman ga hukumar NSCDC ta Jihar Legas da Babban Kwamandan kasa bisa irin kulawa, kauna, da goyon bayan da suka nuna musu a wannan lokaci na bakin ciki.
Ziyarar ta kare ne da sanya hannu a cikin littafin ta’aziyya da Kwamanda Keshinro Adedotun ya yi, inda ya yi addu’a ga Allah Ya jikani marigayin, Ya ba shi hutu mai dadi, tare da bai wa iyalinsa karfin hali da juriya wajen jure wannan babban rashi.




