Hukumar Tsaro ta Najeriya (NSCDC), Kwamandan Jihar Jigawa, ta tabbatar da mutuwar wani yaro mai shekaru 15, Sunusi Abubakar, wanda ya nutse ya mutu a wani tafki da ke kauyen Gabari, gundumar Chamo.
Rahotanni sun bayyana cewa an tsinci gawar yaron a safiyar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, a cikin tafkin da ake kira da “Mahayin Gidan Toro”, wanda ke kimanin kilomita 1.5 arewa da kauyen Gabari.
An gano takalman sa da wandonsa a bakin tafkin da yammacin Talata, 30 ga Satumba, 2025. Mahaifinsa, Abubakar Musa Gabari, ya bayyana cewa Sunusi ya tafi yin wanka a tafkin da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a ranar, amma bai dawo gida ba. Al’ummar yankin suka gudanar da bincike tun daga daren ranar har zuwa safiyar washegari, lokacin da aka gano gawarsa.
An mika gawar ga iyayensa domin yin jana’iza bisa tsarin Musulunci, yayin da babu wata alamar rauni da aka gani a jikinsa.
A cikin wata sanarwa, NSCDC ta jihar Jigawa ta roƙi iyaye, masu kula da yara da shugabannin al’umma su ja hankalin yara da matasa kan hatsarin yin wanka a ruwan buɗe da ba a tabbatar da tsaronsa ba, tare da jaddada muhimmancin tsaro domin guje wa irin wannan mummunar al’amari.
Kwamandan NSCDC na Jihar Jigawa, Muhammad Kabiru Ingawa, ya tabbatar wa al’umma da cewa rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.





