Kwamandan Jihar Katsina na Hukumar Tsaro da Kare Muhimman Ayyuka ta Ƙasa (NSCDC), Kwamandan DM Abbas (Acti, Anim), ya mika takardar shaidar aikinsa ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, a yau Litinin 29 ga Satumba, 2025, a fadar gwamnati ta Muhammadu Buhari House, Katsina.
A yayin ziyarar, Kwamanda Abbas ya isar da sakon gaisuwar fatan alheri daga Babban Kwamandan NSCDC na ƙasa, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, mni, OFR, ga Mai Girma Gwamna. Ya bayyana cewa manufarsa ita ce yin miƙa takardar shaidar aiki tare da jaddada aniyarsa na ɗaukar ingantattun dabaru don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, da kuma kare muhimman kadarorin gwamnati da ababen more rayuwa a cikin jihar.
A cikin jawabin sa, Gwamna Radda ya yi maraba da sabon kwamandan jihar, inda ya tabbatar da cikakken goyon bayan gwamnatin jihar ga hukumar NSCDC wajen yaki da laifuka da miyagun ayyuka. Haka kuma, ya yaba da rawar da hukumar ke takawa wajen yaki da matsalolin tsaro a Katsina.





