Kwamandan Hukumar Tsaro ta Farar Hula da Kare Muhimman Abubuwa (NSCDC) na Jihar Kano, Kwamanda Bala Bawa Bodinga, ya shawarci jami’ai da ma’aikatan hukumar su rungumi dabi’un hakuri, juriya, jajircewa da ladabi wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Yayin da yake jawabi a wurin taron duba dakarun hukumar a hedikwatar Kano, Kwamanda Bodinga ya jaddada muhimmancin ladabi da kwararru wajen aiki. Ya umurci dukkan jami’ai da ma’aikata su kiyaye dokar sanya kayan sutturu ta hukumar, tare da kasancewa cikin tsabta, kyan gani da kuma kwazon aiki a koda yaushe. Haka kuma ya jaddada bukatar a ci gaba da tsaftace harabar hedikwata da kewaye.
Kwamandan ya gargadi jami’ai da ma’aikata da su guji kin zuwa aiki, sakaci da halin ko-in-kula, yana mai cewa ba zai lamunci irin wadannan dabi’u ba a karkashin jagorancinsa. “Jami’ai dole su kasance cikin shiri a duk lokacin da ake bukatar su, musamman idan an kira su don wani aiki. Abin da ya dace ne za a rika yi a koda yaushe,” in ji shi.
Haka kuma ya shawarci jami’an su guji duk wata dabi’a da ka iya kawo musu rashin kwanciyar hankali ko kuma bata sunan hukumar.
A wani bangare, Kwamanda Bodinga ya halarci wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Sabis na Musamman na Jihar Kano, AVM Ibrahim Umar (rtd), ya jagoranta. Taron ya tattauna dabarun magance barazanar tsaro da ke tasowa sakamakon ayyukan hakar ma’adinai a wasu yankunan jihar.





