…Argungu ya gargadi jami’an da suka fadi sau uku za a yi musu ritaya
Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) a ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025 ta gudanar da jarabawar dole ta karin girma ga manyan jami’an ‘yan sanda 30.
Cikin waɗanda suka zauna jarabawar akwai AIG guda ɗaya, CP guda biyu, DCP guda goma sha ɗaya, da ACP guda goma sha shida daga cikin 17 da aka gayyata.
An gudanar da jarabawar a dakin taro na Solomon Arase, bene na shida a hedikwatar hukumar.
Shugaban PSC, DIG Hashimu Argungu (ritaya), ya bayyana wannan shiri a matsayin muhimmin sauyi da zai dawo da kwarewa da mutuncin rundunar. Ya kuma jaddada cewa duk jami’in da ya kasa jarabawar sau uku za a yi masa ritaya a matsayinsa, bisa rashin iya aiki.
Argungu ya bayyana cewa aikin ‘yan sanda a yau yana buƙatar ƙwarewa, don haka duk jami’in da ke son yin gaba a aikinsa dole ne ya dace da bukatun zamani. Haka kuma, ya ce hukumar tana da cikakken kulawa don tabbatar da cewa ba a ba wa mamaci ko wanda ya yi ritaya karin girma ba bisa kuskure.
Taron jarabawar ya samu halartar wasu kwamishinoni na hukumar, ciki har da Mai Shari’a Paul Adamu Galumje (ritaya), Mai Shari’a Christine Ladi Dabup (ritaya), DIG Taiwo Lakanu (ritaya), DIG Uba Bala Ringim (ritaya), da Alhaji Abdulfatah Mohammed.





