Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da su gaggauta daukar mataki don kubutar da Onyesom Udoka, sabuwar lauya da aka sace a kan titin Lokoja–Okene a Jihar Kogi.
An sace Udoka ne a ranar Juma’a tare da ’yar’uwarta da wasu fasinjoji, bayan kammala bikin Call to Bar da ta halarta a birnin Abuja.
A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Shugaban NBA, Afam Osigwe, SAN, ya bayyana wannan lamari a matsayin abin “ƙin yarda da kuma abin tir da tsanani,” yana mai cewa bai kamata kowace iyali ta sha irin wannan mummunan kwarewa a lokacin farin ciki ba.
“Abin tausayi ne cewa a lokacin da ya kamata kasar nan ta rika murnar makomar sana’ar lauya, matasa da iyalansu suna gamuwa da irin wannan tsananin hali,” in ji shi.
NBA ta bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa da haɗin gwiwa, ba kawai domin kubutar da wadanda aka sace ba, har ma domin magance yawaitar matsalar tsaro a manyan hanyoyin Najeriya.
“Ba za a cigaba da daukar lafiyar ’yan Najeriya da wasa ba. Babban aikin gwamnati shi ne kare rayukan jama’a, kuma dole ne a yi hakan da muhimmanci da gaggawa,” sanarwar ta ƙara da cewa.
Rahotanni sun nuna cewa Udoka, wacce ta kammala karatu daga Jami’ar Ambrose Alli da Makarantar Shari’a ta Enugu, tana tafiya ne a cikin motar haya zuwa Benin City lokacin da ’yan bindiga suka kai hari.
Wani abokinta ya wallafa a shafin X (tsohon Twitter) cewa masu garkuwa sun nemi kuɗin fansa na Naira miliyan 20 domin ta da ’yar’uwarta.
Wannan al’amari ya sake haskaka yadda hare-haren garkuwa da mutane ke ƙaruwa a Jihar Kogi. A wannan ranar ma dai, ’yan bindiga sun tare motar fasinja mallakar Big Joe Ventures Ltd, inda suka yi garkuwa da mutane goma sha biyu. Daga baya rundunar ’yan sanda ta jihar ta tabbatar cewa haɗin gwiwar jami’an tsaro da sojoji ya kubutar da mutane takwas, yayin da ana ci gaba da kokarin ceto sauran hudu da ke hannun masu garkuwa.
Kungiyar NBA ta bayyana goyon bayanta ga iyalan Udoka tare da alkawarin tallafa wa kokarin da zai inganta tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa a fadin kasar.




