Jami’an tsaro a Jihar Kwara sun kama mutum biyar da ake zargi da garkuwa da mutane tare da cafke wata babbar kayan maye da aka ɓoye a cikin motar da ke ɗauke da doya.
An samu wannan nasara ne a ranar Juma’a ta hanyar hadin gwiwar jami’an tsaro da suka haɗa da ‘Yan Sanda, Sojojin Najeriya, Ma’aikatan daji, ‘yan sa-kai da jami’an da ke ƙarƙashin Ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Ƙasa (NSA). An tura jami’an tsaron a wuraren da ake yawan samun hare-hare a Kudancin Kwara da Arewacin jihar don dakile garkuwa da mutane da ta’addanci.
Daga cikin wadanda aka kama har da shahararren mai garkuwa da mutane, Tukur Ibrahim daga Tsaragi, wanda ya jagoranci farmakin Babanla a ranar 8 ga Agusta wanda ya kusan tilasta mazauna yankin su bar garin. Sauran da aka kama sun hada da Mohammed Abubakar da Hussain, duk daga Tsaragi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Ejire Adetoun Adeyemi, ta tabbatar da wannan ci gaban cikin wata sanarwa da ta fitar da safiyar Asabar. Ta bayyana cewa a ranar 26 ga Satumba da misalin ƙarfe 4 na yamma, a hanyar Babanla-Oreke-Oke-Ode, jami’an tsaro sun cafke wata mota dauke da doya inda aka gano buhuna 127 na tabar wiwi a ɓoyayyen wuri. An kuma kama mutane biyu, Dan-Teni Haruna da Rabiu Ibrahim, dukkansu daga Saliku, Karamar Hukumar Magama a Jihar Neja, da ake zargin suna da hannu a safarar kayan mayen.
Adeyemi ta kara da cewa ana ci gaba da bincike a kan lamarin, kuma daga karshe za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kwara, Adekimj Ojo, ya yaba wa tawagar hadin gwiwar jami’an tsaro bisa wannan nasara, tare da tabbatar da cewa rundunar ta na da cikakken kudiri wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Ya gargadi masu aikata laifuka da cewa jihar Kwara ba za ta zama mafaka gare su ba.




