Sojojin Ruwa na Najeriya sun bayyana cewa daukar ma’aikata don Makarantar Horar da Sojoji (Basic Training School – BTS) Batch 38 zai gudana daga ranar 2 ga Oktoba zuwa 31 ga Oktoba, 2025. Rundunar ta jaddada cewa tsarin neman aikin kyauta ne, kuma dukkan masu nema za su cike fom dinsu ta yanar gizo a shafin hukuma: www.joinnigeriannavy.navy.mil.ng. Duk wanda ya yi nasara za a kai shi horon soja na farko kafin a kaddamar da shi a matsayin Ordinary Seaman.
Cancanta ta takaita ne ga ‘yan Najeriya ta haihuwa masu sahihin Lambar Shaida ta Ƙasa (NIN). Masu nema ba za su kasance da wani tarihin aikata laifi ba, kuma ba za su kasance cikin kowace ƙungiyar asiri, tsafi ko ƙungiyoyin da doka ba ta amince da su ba. Rundunar ta bayyana sharuddan ilimi da shekaru kamar haka: masu neman aiki da sakamakon O’level dole su kasance tsakanin shekara 18 zuwa 22 zuwa 31 ga Disamba, 2025. Masu neman aiki da takardar OND/NCE dole su kasance tsakanin shekara 18 zuwa 26, yayin da Chaplain/Imam Assistants da Direbobi/Mekanik za su kasance tsakanin shekara 18 zuwa 28. A kowane hali, duk masu nema dole su sami aƙalla darussa biyar da suka yi nasara da cikakken sakamako, ciki har da Turanci da Lissafi, a ba fiye da zama biyu na WAEC, NECO, GCE ko NABTEB, tare da shaidar da ba ta wuce shekara 2015 ba.
Masu neman aiki a fannoni na musamman irin su Medical Assistants da Nurses dole ne su gabatar da shaida daga hukumomin kwararru da ke da alhakin rijista. Masu neman aiki a fannoni na sana’o’in hannu – kamar ɗinki, famfo, aikin gini da katako, walda, da lantarki – dole ne su gabatar da Trade Test Certificates tare da sakamakon karatunsu. Haka kuma, ‘yan wasa ma suna da damar neman shiga, amma dole su gabatar da shaida ta lambobin yabo ko takardu da suka nuna nasarorinsu. Rundunar ta ayyana ranar 29 ga Nuwamba, 2025 a matsayin ranar gudanar da jarabawar shiga a wurare da aka tanada a fadin ƙasa. Duk masu nema dole ne su zo da Attestation Form da aka sanya hannu tare da hoton mai sa hannun, da kuma wata sahihiyar shaida kamar Lasisin Tuƙi, Fasfo ko Katin Shaida na Ƙasa.
Sojojin Ruwa sun gargadi masu nema cewa yin amfani da fom fiye da daya zai kai ga soke cancanta, sannan sun jaddada cewa tambayoyi da neman ƙarin bayani za a aika su ne kawai ta tashoshi na hukuma da aka bayar a shafin yanar gizo na daukar ma’aikata.





