Hukumar Tsaro ta DSS (Department of State Services) ta yi nasarar ceto yara 25 da aka yi garkuwa da su a unguwar Sabon Layi da ke Karamar Hukumar Wase a Jihar Filato. An mika yaran da aka ceto din a hukumance ga Gwamnatin Jihar Filato a garin Jos a ranar Asabar.
Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Samuel Jatau, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya yaba wa hukumar DSS bisa gaggawa da kwarewar da suka nuna wajen shiga tsakani. Ya ce nasarar wannan aiki ya nuna irin jajircewar da hukumomin tsaro ke da shi wajen kare rayuka, musamman na yara kanana marasa karfi.
A cewar Jatau, an sace yaran ne a ranar 21 ga watan Disamba, 2025, yayin da suke kan hanyar tafiya don halartar bikin Maulidi. Ya bayyana cewa masu garkuwar sun yi shigar ‘yan banga ne kafin su tare yaran su kuma yi awon gaba da su.
Ya bayyana cewa bayan faruwar lamarin, DSS ta kaddamar da bincike da farauta mai tsanani wanda a karshe ya haifar da ceto dukkan yara 25 lami lafiya ba tare da an rasa rai ko wani ya jikkata ba. Ya lura cewa an gudanar da aikin ne cikin matukar kwarewa da sanin makamar aiki.
Jatau ya kara da cewa yaran, wadanda suka kunshi mata shida da maza 19, sun riga sun wuce ta gwajin lafiya kuma an tabbatar suna cikin koshin lafiya. Ya kara da cewa ana kan shirye-shiryen mayar da su ga iyalansu, yayin da gwamnatin jihar ke ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro don hana sake faruwar irin hakan nan gaba.




