Sojojin 6 Brigade na Rundunar Sojin Najeriya Sector 3 Operation Whirl Stroke sun samu muhimman nasarori a fagen aiki karkashin Ayyukan Peace Shield da Zafin Wuta, inda suka kaddamar da jerin hare hare na tsaro da suka haifar da tarwatsa fashi, ceto mutanen da aka sace, da kwato makamai a wasu yankuna dabam dabam na Jihar Taraba.
A ranar 6 ga Disamba 2025, sojojin da ke Manya sun yi gaggawar mayar da martani bayan samun kiran gaggawa cewa yan fashi sun toshe hanyar Manya zuwa Takum suna kwace kayayyaki daga masu tafiya. Sojojin suka dauki mataki nan take suka kaddamar da aikin kawar da barazana. Da zarar miyagun suka hango sojojin na matsowa, suka tsere cikin rudani suka bar makaman su. Binciken da aka yi ya kai ga kwato bindiga AK 47 guda daya, mazagin AK 47 guda daya, da harsashi 7.62mm Special guda uku. Wannan matakin ya hana afkuwar barna kuma ya dawo da zirga zirga yadda ya kamata a hanya.
A wani samame dabam da aka gudanar a ranar 7 ga Disamba 2025, sojojin da ke Kufai Amadu sun samu sahihin bayanai cewa wasu maza hudu daga Bauchi masu tafiye tafiya da babura biyu an sace su a cikin garin Amadu yayin da suke kan hanyarsu zuwa Baissa a Karamar Hukumar Kurmi. Bincike na farko ya nuna cewa mutanen masu bako a yankin sun tsaya su tambayi hanyar ne lokacin da Musa Danji da Yusuf suka fada hannun masu garkuwa da su suka yi gaba da su zuwa New City. Sojojin suka kaddamar da gaggawar aikin bincike da ceto.
A yayin share dazuzzukan yankin, sojoji sun samu nasarar ceto wasu daga cikin mutanen da aka sace Yusuf Musa da Muhammed Umar bayan sun tsere daga hannun masu garkuwa. Bincike yana ci gaba domin gano sauran wadanda aka sace Musa Danji da Yusuf, yayin da ake kara tsananta bincike don kama masu laifin.
Haka zalika, a ranar 6 ga Disamba 2025, sojojin da ke Iware, bisa bayanan sirri, sun gudanar da aikin bincike a Garin Sambo kauyen Tau a Karamar Hukumar Ardo Kola. A yayin aikin, sojoji sun kwato bindigogi Pump Action guda biyu, harsashi goma sha uku, babura biyu, da wayoyin Tecno hudu. An kama mutane biyu Baba Wura Sambo da Mallam Adamu Darda a zargin mallakar makamai ba bisa kaida ba. Dukkan mutanen da aka kama tare da kayayyakin da aka kwato suna hannun soji domin karin bincike.
Kwamandan 6 Brigade Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa ya yaba da jajircewa, kwarewa da gaggawar amsa kiran da sojoji suka nuna. Ya nanata kudirin rundunar wajen ci gaba da kai hare haren kawar da barazana karkashin Operation Peace Shield da Operation Zafin Wuta domin tabbatar da Taraba ta tsira daga duk wani nauin laifuka.
Ya kuma tabbatar wa jama a da matafiya musamman a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara cewa rundunar ta himmatu wajen tabbatar da tsaron manyan hanyoyi da alummomi domin samar da zirga zirgar lafiya ba tare da tangarda ba.
Janar Uwa ya kuma yi kira ga jama a su kasance masu lura tare da ci gaba da bada sahihan bayanai ga jami an tsaro domin taimakawa wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.



