Hukumar Tsaro da Kare Jama’a ta Najeriya (NSCDC), Jihar Sokoto, ƙarƙashin jagorancin Kwamanda Emmanuel A Ajayi, ta sake nanata kudirinta na kare rayuka da dukiyoyi ta hanyar ƙarfafa haɗin kai da aiki tare da al’ummomi a duk faɗin jihar.

A cikin wani sabon yunƙuri na yaki da matsalolin tsaro ta hanyar haɗa kai da al’umma, tattara sahihan bayanan tsaro, da kuma inganta tsarin tsaron ƙasa na gida, NSCDC tare da al’ummar Torankawa sun kaddamar da sabon ofishin aiki da aka gina a ƙauyen Torankawa, cikin Karamar Hukumar Yabo, a ranar Juma’a 28 ga Nuwamba 2025 da misalin ƙarfe 09:00 na safe.
Kafa wannan sabon ofishin wani muhimmin ɓangare ne na shirin hukumar na faɗaɗa kasancewar jami’an tsaro, ƙara aminci a cikin al’umma, da farfaɗo da tsarin tsaro ta hanyar ingantaccen sintiri, tattara bayanan leƙen asiri, da gaggauta ɗaukar mataki a lokutan gaggawa a Torankawa da makwabtanta.
A jawabinsa yayin bikin kaddamarwar, Kwamanda Ajayi ya yaba wa karamci, haɗin kai da hangen nesan al’ummar Torankawa. Ya bayyana aikin a matsayin hujjar jajircewar jama’a wajen zaman lafiya, ci gaba da ɗaukar nauyin tsaro tare.
“Tsaro nauyi ne da ya shafi kowa. Yana buƙatar tsari na gari da cikakken dabaru. Muna godiya ƙwarai ga al’ummar Torankawa bisa irin goyon bayan da suka bayar. Za mu tabbatar an samar da dukkan kayan aiki da isassun jami’ai a wannan ofishi domin su rika mayar da martani cikin gaggawa,” in ji shi.
Kwamanda Ajayi ya ƙara bayyana cewa kafa ofishin na daidaita da hangen nesa na Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Abubakar Ahmed Audi, mni, OFR, na kusantar da ayyukan tsaro ga jama’a tare da ƙarfafa zumunci da musayar bayanan sirri tsakanin hukumar da al’ummomi a fadin ƙasar.
Wakilin Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Torankawa, ya yaba wa NSCDC bisa irin kwazon da take nunawa a aikin tsaron al’umma, inda ya bayyana kwarin gwiwa cewa sabon ofishin zai taimaka sosai wajen rage laifuka da matsalolin tsaro a yankin.
Haka kuma, wakilin Shugaban Karamar Hukumar Yabo, Alhaji Usman Na Allah, ya jinjinawa wannan mataki tare da yin alkawarin ci gaba da goyon bayan karamar hukumar ga duk wasu shirye shiryen tsaro da za su kawo zaman lafiya, haɗin kai da cigaba.
Bikin kaddamarwar ya ja hankalin sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da sauran muhimman masu ruwa da tsaki, waɗanda suka yi alkawarin ci gaba da haɗin kai domin samun nasarar wannan ofishi da kuma ƙarfafa tsarin tsaro a yankin.



