Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya soki yadda Gwamnatin Tarayya ta nuna farin ciki kan sakin ’yan matan da aka sace a Jihar Kebbi, yana mai cewa sakin nasu ba nasara ba ce, illa kuwa karin hujja kan tabarbarewar tsaron Najeriya.
A wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar a ranar Laraba, Atiku ya ce dawowar yaran lafiya “ba wani abin alfahari ba ne” sai dai tunatarwa mai tayar da hankali cewa kungiyoyin ta’addanci yanzu suna aiki a fili, suna tattaunawa ba tare da tsoro ba, suna kuma tsayar da sharudda yayin da jami’an gwamnati ke sakin bayanai domin kare mutuncinsu. Jawabinsa ya mayar da martani ne kan kalaman mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, a wata hira da ya yi da Arise News TV ranar Litinin.
Onanuga ya yabawa hukumar DSS da sojoji bisa rawar da suka taka wajen bin sawun masu garkuwa da mutane a ainihin lokacin faruwar lamarin tare da samun damar tattaunawa da su har aka ceto yaran ba tare da an biya kudin fansa ba. A cewarsa, ko da yake jami’an tsaro suna da bayanan sirri masu karfi, sau da yawa ba su iya kai hari kai tsaye saboda hadarin da hakan zai iya haifar wa kan fararen hula da ke hannun ’yan bindigar.
Ya ce jami’an tsaro sun san mutanen da ke aikata laifukan a yankin, sun san inda suke, amma dole su yi taka-tsantsan don kada su jawo mutuwar bayin Allah marasa laifi.
Atiku ya karyata wannan hujja, yana mai cewa hakan yunkuri ne na rufe gazawar gwamnati da fakewa da jarumta. Ya tambaya dalilin da ya sa, idan da gaske jami’an tsaro suna iya bin diddigin masu garkuwa da mutane a ainihin lokacin, ba su kama su ko kawar da barazanar ba. Ya ce abin takaici ne ganin gwamnati na alfahari da tattaunawa da ’yan ta’adda maimakon kawo karshen su. Ya kuma nuna damuwa cewa garkuwa da mutane yanzu kamar cinikayya ce tsakaninsu da gwamnati.
Ya kara da cewa bayanan gwamnati suna nuna kamar ’yan ta’adda da barayi sun zama wata gwamnati dabam, suna tattaunawa, suna karbar kudin fansa, sannan suna tserewa ba tare da an hukunta su ba, yayin da fadar shugaban kasa ke murna da abin da ya kira “hadin kai.” Ya ce babu wata kasa mai hankali da za ta yaba kanta saboda tattaunawa da ’yan bindiga da take ikirarin tana sa ido a kansu.
Sace ’yan matan ya faru ne a ranar 17 ga Nuwamba, lokacin da ’yan bindiga suka afka makarantar Government Girls’ Secondary School da ke Maga, Jihar Kebbi, suka kashe ma’aikaci daya sannan suka sace dalibai 25 daga dakunan kwanan su. Daya daga cikinsu ta tsere jim kadan bayan haka, abin da ya rage 24 a hannun ’yan bindigar har zuwa ranar Talata da aka sako su.
Shugaba Bola Tinubu ya yi maraba da labarin, yana mai cewa ya yi farin ciki da tabbatar da cewa an nemo duka ’yan mata 24. Ya yabawa jami’an tsaro bisa kokarinsu tare da umartar karin tura jami’ai zuwa yankunan da ke fama da matsalolin tsaro. Ya kuma bukaci jami’an tsaro da su hanzarta ceto sauran mutanen da ke hannun ’yan bindiga a sassan kasar.
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya tabbatar da cewa ba a biya kudin fansa ba, yana mai cewa hadin gwiwar jami’an tsaro ne da hukumomin jihar ya taimaka wajen sakin ’yan matan.





