Kwamitin Ƙananan Harkokin Afirka na Majalisar Wakilan Amurka yana shirin gudanar da babban zaman sauraron jama’a a ranar Alhamis, 20 ga Nuwamba, 2025, domin duba matakin da Shugaba Donald Trump ya ɗauka na mayar da Najeriya cikin jerin Kasashen da ke da Matsaloli na Musamman (CPC) sakamakon zargin cin zarafin ‘yancin addini. Idan Majalisar Dattawa ta amince da wannan matsayin, zai iya kai ga kakabawa jami’an Najeriya takunkumi tare da takaita wasu nau’o’in tallafin Amurka.
Za a gudanar da zaman ne da ƙarfe 11:00 na safe a ɗakin 2172 na ginin Rayburn House Office Building, ƙarƙashin jagorancin Chris Smith (R-NJ), kuma za a watsa shi kai tsaye ga jama’a. Za a sami kwamitoci biyu na shaidu, ciki har da manyan jami’an Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da fitattun shugabannin addini daga Najeriya.
A cewar gayyatar da aka aika wa mambobin Kwamitin Harkokin Kasashen Waje, shaidu da ake sa ran su gabatar da jawabi sun haɗa da Jonathan Pratt, babban jami’in Hukumar Harkokin Afirka; Jacob McGee, Mataimakin Sakataren Ma’aikatar Dimokuraɗiyya, ‘Yancin Dan Adam da Ma’aikata; Ms. Nina Shea daga Cibiyar ‘Yancin Addini; Bishop Wilfred Anagbe na Cocin Katolika ta Makurdi; da Ms. Oge Onubogu daga Cibiyar Nazarin Tsare-Tsare da Harkokin Duniya.
Zaman zai tattauna kan zargin cin zarafin ‘yancin addini a Najeriya, ya duba yiwuwar matakan siyasar Amurka irin su takunkumin musamman, tallafin jin ƙai, da matakan haɗin gwiwa tsakaninsu da hukumomin Najeriya wajen dakile hare-hare masu ƙara ta’azzara. Wannan na zuwa ne bayan sanarwar Trump ta 31 ga Oktoba, 2025, inda ya mayar da Najeriya cikin jerin CPC, matakin da ya haifar da mahawara a tsakanin diflomasiyoyi da shugabannin addinai.
Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar “barazana ga wanzuwarsu,” yana danganta mutuwar dubban mutane ga kungiyoyin tsattsauran ra’ayi. A wata sanarwa da ya fitar a ranar 1 ga Nuwamba, ya gargadi cewa Amurka na iya dakatar da duk wani tallafi ga Najeriya, ko ma ta yi tunanin ɗaukar matakin soja idan gwamnatin Najeriya ta kasa shawo kan kashe-kashen. Ya umarci Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka ta fara shirin yiwuwar shiga tsakani, yana bayyana yiwuwar wannan matakin da cewa “zai kasance da sauri, da ƙarfi, kuma ba tare da ɓata lokaci ba.”
Shugaba Bola Tinubu ya musanta ikirarin Trump cikin gaggawa, yana mai cewa Najeriya ƙasa ce da ta gindaya ‘yancin addini a cikin kundinta na tsarin mulki. A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce kalaman Trump ba su dace da hakikanin tsarin addinai iri-iri na Najeriya ba, yana mai cewa juriya da ‘yancin bauta sune ginshiƙai na ƙasar.
Sake sanya Najeriya a jerin CPC ya zo ne a lokacin da ake cigaba da rahotannin hare-haren da ake kai wa al’ummomin Kirista, ciki har da kashe-kashe, garkuwa da mutane, da kona majami’u da ake danganta wa ‘yan ta’adda da kuma makiyayan Fulani masu ƙungiyoyi. Wani kudiri da ke da alaƙa da wannan batun, wanda Sanata Ted Cruz ya dauki nauyi, yana gaban Majalisar Dattawan Amurka.
Bishop Anagbe, ɗaya daga cikin muhimman shaidu a zaman Majalisar, ya taba gabatar da irin waɗannan korafe-korafe a gaban ‘yan majalisar Burtaniya a ranar 25 ga Maris, 2025, inda ya bayyana yadda ake kashe Kiristoci tare da korar su daga gidajensu a Jihar Benue. Ya ce an ƙona kauyuka, an kwace gonaki, an lalata coci-coci, kuma an kashe limamai da mutane masu bin addini — har ma da waɗanda suka samu mafaka a sansanonin ‘yan gudun hijira.
A cewarsa, “Wadannan hare-hare na biyo bayan umarni ne na mamaye, kashewa, da kwace ƙasa,” yana mai cewa ana kai wa al’ummomi marasa kariya hare-hare ba tare da jin tsoron hukunci ba. Ana sa ran bayaninsa zai taka rawar gani wajen tantance matsalar da kwamitin majalisar Amurka zai yi yayin da ƙasar ke ƙara bibiyar batutuwan cin zarafin ‘yancin addini a duniya.



