Hukumar Tsaro ta ‘Yan Sanda na Farar Hula ta Ƙasa (NSCDC) reshen Jihar Kogi ta kaddamar da sabon Sashen Ofante, bisa ga hangen nesa da manufofin Babban Kwamandan Hukumar, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, mni, OFR, domin inganta tsaro tun daga matakin ƙasa. Wannan mataki yana nufin ƙarfafa ikon hukumar wajen kare rayuka, dukiyoyi, da kuma Muhimman Kadarori da Ababen Gina Ƙasa (CNAI) a fadin jihar.
Kwamandan Jihar Kogi, Aletan Olumide E., ne ya jagoranci wannan shiri, inda ya tabbatar da ɗaukaka Ofante Outpost zuwa cikakken Ofishin Sashen NSCDC, wanda ya cika dukkan ƙa’idoji da matakan da ake buƙata. Ofishin yana cikin Karamar Hukumar Olamaboro ta Jihar Kogi, kuma yankin Ofante yana iyaka da Jihar Anambra, Benue, da Enugu, wanda hakan ke sa wannan wuri ya zama mai matuƙar muhimmanci wajen gudanar da tsare-tsare da amsa gaggawa ga al’umma.
A yayin bikin kaddamarwar, Babban Malami kuma Jagoran Al’umma, Chief Elder Dr. Ogwu Onoja (SAN), ya yabawa hukumar NSCDC bisa gagarumar rawar da ta taka wajen inganta tsaro a yankin. Ya ce an samu raguwa sosai a ayyukan ta’addanci tun bayan zuwan hukumar, yana mai jinjina wa jajircewarsu da ƙoƙarin da suke yi. Ya kuma bukaci hukumar da ta ci gaba da nuna jajircewa tare da ƙarfafa haɗin kai da al’umma.
A nasa jawabin, Kwamanda Aletan Olumide ya gode sosai ga Elder Dr. Ogwu Onoja James (SAN) bisa goyon baya da gudunmawar da ya bayar wajen gina da kuma samar da kayan aikin ofishin kafin miƙa shi ga hukumar NSCDC. Ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin jami’an hukumar da al’ummar yankin domin tabbatar da aiwatar da ayyuka cikin nasara da kare rayuka, dukiyoyi da kadarorin gwamnati.
Kwamandan ya kuma yi gargaɗi mai tsanani ga duk wanda ke da niyyar aikata laifi ko taimaka wa masu laifi da ya daina nan da nan, domin hukumar za ta ɗauki matakin doka ba tare da nuna bambanci ba. Ya tabbatar da cewa NSCDC za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, adalci, da tsaro ga kowa da kowa cikin gaskiya da ƙwarewa.



