A ci gaba da aiwatar da manufarta na ƙara wayar da kan jama’a da kuma ƙarfafa sanin dabarun hana gobara a fannoni daban-daban, Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa (Federal Fire Service – FFS) ta sanar da wani muhimmin haɗin gwiwa da masana’antar nishaɗi ta Najeriya, wanda zai fara ne da bikin “The 2Baba Experience” da za a gudanar a ranar Jumma’a, 14 ga Nuwamba, 2025, a Transcorp Hilton, Abuja.
Wannan shiri ya biyo bayan ziyarar ban girma da fitaccen mawakin Najeriya kuma jakadan zaman lafiya na duniya, Innocent “2Baba” Idibia, ya kai wa Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa, Olumode Adeyemi Samuel, FCNA, ACTI, a hedkwatar hukumar da ke Abuja.
Manufar ziyarar ita ce neman haɗin gwiwar hukumar da kuma tallafin ƙwararrunta domin tabbatar da tsaron wurin taron da kuma shirye-shiryen gaggawa yayin bikin cikar 2Baba shekaru 25 a harkar waka.
Da yake maraba da mawakin da tawagarsa, Shugaban Hukumar ya yaba wa 2Baba bisa rawar da yake takawa wajen ci gaban matasa, ƙarfafa zaman lafiya da gina ƙasa ta hanyar kiɗa. Haka kuma ya jinjina masa saboda yunkurinsa na haɗa batun tsaron jama’a da wayar da kan mutane kan hanyoyin kare gobara a cikin babban taron nishaɗi kamar wannan.
A cikin wannan haɗin gwiwar, Hukumar Kashe Gobara za ta tura tawagar ma’aikata da motocin kashe gobara zuwa wurin taron domin tabbatar da bin ƙa’idodin tsaro yadda ya kamata. Haka kuma za a gudanar da binciken tsaro kafin taron, kimanta haɗarin gobara, tare da tsayawa cikin shiri don amsa duk wata gaggawa a lokacin bikin.
A nasa jawabin, 2Baba ya gode wa Shugaban Hukumar da dukkan jami’an hukumar saboda ƙwarewarsu da kuma shirin yin aiki tare da masana’antar nishaɗi. Ya jaddada muhimmancin sanya tsaro a gaba duk lokacin da mutane ke taruwa don murnar wani abu.
“Kiɗa na haɗa mutane wuri guda, amma tsaro ne ke tabbatar da farin ciki yana dorewa,” in ji 2Baba. “Haɗin gwiwa da Hukumar Kashe Gobara na ba ni tabbacin cewa wannan biki zai kasance abin tunawa, cikin tsaro da kuma cike da farin ciki ga kowa da kowa.”




