Sabon Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Muhimman Abubuwan Gwamnati (NSCDC) na Jihar Kano, Kwamanda Mohammed Hassan Agalama, ya karɓi ragamar mulki a yau a Hedikwatar Hukumar da ke Kano, bayan an tura shi zuwa wannan matsayi ta hannun Babban Kwamandan Hukumar, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, mni, OFR. Wannan canjin ya kasance wani ɓangare na kokarin da hukumar ke yi don ƙarfafa aikin tsaro da inganta tsarin tsaron cikin gida a fadin ƙasa.
A jawabin sa na farko ga jami’ai da manema labarai, Kwamanda Agalama ya bayyana godiyarsa ta musamman ga Babban Kwamandan Hukumar bisa amincewar da ya nuna masa. Ya kuma tabbatar da cikakken jajircewarsa wajen aiwatar da manyan ayyukan hukumar, wadanda suka haɗa da kare muhimman kadarorin ƙasa da gine-gine, kula da bala’o’i, yaƙi da masu lalata dukiyar gwamnati, da kuma warware rikice-rikicen al’umma ta hanyar zaman lafiya.
Kwamandan ya tabbatar wa jama’ar Jihar Kano cewa, karkashin jagorancinsa, hukumar za ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kare rayuka da dukiyoyi, domin samar da yanayi mai kyau ga cigaban tattalin arziki da walwalar al’umma.
Haka kuma, Kwamanda Agalama ya jaddada muhimmancin huldar aiki tsakanin hukumomin tsaro, hadin kan al’umma, raba bayanan sirri, da daukar mataki cikin gaggawa kan barazanar tsaro. Ya bukaci goyon baya da hadin kai daga sauran hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, kafafen yada labarai, da al’umma baki ɗaya domin cimma nasarar hukumar.
Yayin da yake sake jaddada manufar hukumar ta rashin amincewa da rashawa, rashin ladabi, da aikata ba daidai ba, Kwamandan ya ce zai tabbatar da cewa dukkan jami’ai da ma’aikata karkashin kulawarsa za su kasance



