Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) reshen Jihar Katsina ta tabbatar da sabunta haɗin gwiwarta da Hukumar Harajin Shige da Fice ta Najeriya (NCS) domin ƙara inganta harkokin tsaro, tabbatar da zaman lafiya, da kare muhimman kadarorin kasa da manyan gine-gine.
An sake nanata wannan kudiri ne a lokacin da Kwamandan Jihar, CC A.D. Moriki (Mai Rikon Mukami), ya kai ziyarar ban girma ga Mai Kula da Yankin Hukumar Kastam, Kwamptrola Abba-Aji Idris, a ranar Talata, 4 ga Nuwamba, 2025, a Hedikwatar Hukumar Kastam dake Katsina.
A yayin ziyarar, Kwamanda Moriki ya bayyana cewa wannan ganawa na da nufin ƙarfafa kyakkyawar alaƙa da ke tsakanin hukumomin biyu a Jihar Katsina. Ya yaba da jagoranci da hangen nesa na Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, mni, OFR, wanda yake ci gaba da tallafawa ƙoƙarin tsaron ƙasa da kare muhimman wuraren gwamnati.
Kwamanda Moriki ya kuma bayyana kudurinsa na ci gaba da haɗin kai mai ƙarfi da Hukumar Kastam ta hanyar musayar bayanan sirri, gudanar da hadin gwiwar ayyuka, da wayar da kan jama’a domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar. Ya gode wa Hukumar Kastam bisa kyakkyawan tarba da kulawa da aka nuna masa da tawagarsa.
A nasa jawabin, Kwamptrola Abba-Aji Idris ya yi maraba da sabon Kwamandan Jihar tare da yaba wa NSCDC bisa jajircewarta wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro. Ya tabbatar da cewa Hukumar Kastam za ta ci gaba da yin aiki tare da NSCDC domin yaki da fasa kwauri, karfafa tsaron iyakoki, da magance miyagun laifuka na kan iyaka da ke barazana ga tsaron jama’a.
Hukumomin biyu sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da yin aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban kasa baki daya.




